Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Makon da ya gabata ya kasance wani matsanancin lokaci ne da mafi akasarin ‘yan Nijeriya musamman mu al’ummar Arewa, za mu daɗe ba mu manta da shi ba, sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar, da yadda ta rikiɗe zuwa tarzoma da ɓarnatar da dukiya, har ma da asarar rayuka da aka samu a wasu wuraren. Jihohi da dama sun kasance ƙarƙashin dokar zaman gida ta tsawon awoyi da gwamnatocin jihohin suka kafa domin daƙushe zafin da tarzomar ta yi, da taƙaita bazuwarta. Abubuwa da dama da muka yi hasashen aukuwarsu a lokacin zanga-zangar, matuƙar ba a ɗauki matakan da suka kamata ba, mun ga sun faru, har ma da waɗanda ba mu yi tunanin za su iya faruwa ba. Kamar misalin, ƙoƙarin ƙwace motar ’yan sanda mai sulke da masu tarzoma suka yi a Kaduna, da wasu makamai da aka ɗauke a wajen ’yan sanda a Kano. Sai kuma amfani da tutar ƙasar Rasha da wasu suka yi a Kano, Katsina da Kaduna da wasu wurare a lokacin zanga-zanga.
Kamar yadda aka yi zargi, akwai alamun ’yan sanda a wasu jihohi sun yi amfani da ƙarfi fiye da kima kan masu zanga-zanga, wanda ya hassala wasu matasa wajen farwa jami’an tsaro da fashe-fashen kayan gwamnati. Sannan akwai batun tsorata jagororin zanga-zanga, da farautarsu da jami’an tsaro suka riƙa yi ya sa su janye jikinsu daga shiga zanga-zangar a zahiri, sai aka bar wasu tsagera da suka jagoranci mayar da zanga-zangar lumana zuwa ta tarzoma. Waɗanda suka yi kyakkyawan tsari don ganin sun isar da saƙo, kuma an yi zanga-zanga cikin lumana, daga baya an bar su da cizon yatsa, saboda ganin abubuwa sun taɓarɓare ba kamar yadda suka yi zato ba.
Akwai alamun gwamnati da jami’anta sun yi amfani da wasu dabaru na hana zanga-zangar tasiri a wasu yankuna na ƙasar nan, da ƙirƙirar wani gungu na masu zanga-zanga masu goyon bayan gwamnati da suka ƙalubalanci masu zanga-zangar tsadar rayuwa. A jihohi irinsu Adamawa, da Taraba, da Filato har da Babban Birnin Tarayya Abuja, har ma da bayyanawa manema labarai jerin wasu ƙungiyoyi da aka yi amfani da su wajen nuna janyewarsu daga masu zanga-zanga, kamar yadda ake so a nuna hankalin ’yan ƙasa ba a haɗe yake ba. Mun ga yadda aka yi amfani da masu shirya fina-finai da mawaƙa wajen fahimtar da matasa rashin dacewar yin zanga-zanga ta ayyukan da suke yi, a cikin tallace-tallacen talabijin da kafafen sada zumunta, da kuma ta waƙe-waƙe. Duk waɗannan abubuwa ne da za a ce gwamnati na da damar yin su musamman idan ta fahimci barin masu zanga-zanga su ci karensu babu babbaka, na da illa ga kimar gwamnati da tasirinta.
Wani abu kuma da ya ja hankalina a yayin wannan zanga-zanga shi ne yadda wasu matasa a wasu wurare suka riƙa nuna sun fi son sojoji su hamɓare gwamnatin Shugaba Tinubu su karɓi mulki, kamar yadda muka gani a wasu bidiyoyi da suke yawo a wayoyin jama’a, daga Jos da Sakkwato. Yayin da maboya bayan ra’ayin malamai ke ta bayyana cewa, ai lalacewar tasirin zanga-zanga na da nasaba da bijirewa nasihar malamai ne. Suna masu cewa, ai dama abin da babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba!
Jawabin shugaban ƙasa na ranar Lahadi game da zanga-zangar matsin rayuwa ya sake harzuƙa masu zanga-zanga, inda a garuruwa da dama muka ga ƙaruwar matasa maza da mata a titi suna bayyana rashin jin daɗin su da kalaman da shugaban ƙasa Tinubu ya yi amfani da su. Kalaman da suka ce basu taɓa muhimman abubuwan da suka fitar da su zanga-zanga kan titi ba, bugu da ƙari ma kuma ƙara jaddadawa da ya yi babu batun dawo da tallafin man fetur, kamar yadda jama’a suka sa rai za su ji. Matasa a Kaduna, Zariya da Jos inda ake ganin an yi abin a yaba, sakamakon yadda zanga-zanga a kwanakin farko ta gudana cikin lumana, sun fusata kan titi suna nuna rashin jin daɗinsu, da kuma far wa kamfanoni da rumbunan adana abinci suna fasawa don ɗiban ganimar kayan abinci, kamar yadda suka ga ya faru a Kano. Kodayake ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi na kwantar da tarzoma, da hana ɓata-gari fasa wuraren kasuwancin jama’a a wurare da dama, ya taimaka ainun wajen hana watsuwar ɓarna da rashin bin doka.
Duba da dukkan abubuwan da suka wakana, a inda zanga-zanga ta yi tasiri, da inda ɓata-gari suka yi wa jama’a da gwamnati ɓarna, za a iya cewa ‘yan Nijeriya sun furzar da abin da ke ransu, game da tsadar rayuwa da yunwa, taɓarɓarewar tsaro, da cin amanar ƙasa daga jami’an gwamnati da sauran abubuwa na rashin gaskiya da suke faru a gwamnatance. Kuma kamar yadda shugaban ƙasa da kansa ya jaddada, gwamnati ta saurari koke-koken jama’a ƙarara, kuma tana ɗaukar matakan da suka dace na kawo sassauci a rayuwar talakawan ƙasar nan. Lallai ne gwamnati ta tabbatar ta cika wannan alƙawari, domin jama’a su ga canji a rayuwarsu da ta iyalinsu. Ya kamata Gwamnati ta duba yiwuwar samar da tallafi ga kayan abinci da magunguna, ba a dakatar da harajin shigo da su na watanni shida kawai ba. Gwamnati ta ɗauki nauyin shigo da su da sayen na cikin gida a sayar wa talaka cikin rahusa, wannan zai taimaka wajen sassauta ƙuncin da talaka ke ciki.
Idan muka ɗauke batun ɓarnar dukiya da sace-sacen kayan jama’a da na gwamnati, da kuma asarar rayuka da aka samu, wanda muka yi tir da Allah wadai da su, za a iya cewa talakawan Nijeriya sun yi amfani da ‘yancinsu da tsarin mulkin dimukraɗiyya ya ba su na bayyana rashin jin daɗinsu da yadda ake tafiyar da al’amarin shugabanci a ƙasar nan, wanda ke ƙara sa rayuwar jama’a cikin ƙunci da wahala. Kuma ya zama ƙalubale ga mahukunta a dukkan matakai su tabbatar sun yi abin da ya dace, nan kusa ba sai wani lokaci nan gaba ba!
Kamar yadda na ga wani matashi da ya fito zanga-zanga a ranar farko ya rubuta a jikin kwalin da ya ɗaga yana cewa, A BAMU ABINCI KAWAI. Wannan fa shi ne babbar matsalar talakan Nijeriya, ya kamata gwamnati ta lura da wannan, ba dogon turanci muke so ba!
