Daga ABDULLAHI JIBRIL LARABI (UNCLE LARABI)
Binciken da na gudanar game da tsadar kayan masarufi, musamman kayan abinci a Nijeriya, ba laifin gwamnati ba ne kaɗai. Ya haɗa har da laifin ’yan kasuwa da talakawan Arewacin Nijeriya.
Dalilina kuwa na faɗin hakan shine, binciken da na yi tsahon wata guda akan me ke haifar da tsadar kayan abinci a Nijeriya bayan kuma da yawan wasu daga cikin kayan abincin a ƙasarmu ake nomawa, ya tabbatar min da cewar, ’yan kasuwa da talakawa na tururuwar fitar da abincin ne maƙotan ƙasashen da suke kusa da mu, inda kuɗinsu ke da daraja fiye da kuɗin Nijeriya, irinsu Nijar, Chadi, Kamaru, Kwatano (Benin), Togo da sauran ƙasashen Africa.
Yayin da wasu kuma a nan gida Nijeriya suke safarar abincin zuwa Kudancin ƙasar nan, inda suke sayar da abincin da tsada ninkin yadda ake siyarwa a Arewacin ƙasar nan, hakan shi ya ke haifar da ƙaranci da kuma tsadar kayan abincin a Arewacin ƙasar nan da ma Nijeriya bakiɗaya.
Kiran da zan yi ga gwamnati shine, tunda ta haramta shigo da kayan abinci har bin mutanen da suke shigo da kayan abincin take ta harbe, to ya kamata ta sanya doka mai tsanani wajen hana fita da kayan abincin. Hakan shi zai sanya abincin ya yawaita kuma ya sauƙaƙa yadda kowa zai iya sayen abinci cikin daɗin rai.
Amma abin haushi da takaici ne ana noma kayan abinci a ƙasarmu Nijeriya kayan su riƙa gagarar talaka saye ya ci, saboda tsada da kuma ƙarancinsa. Kowa ya san a Arewa mu na noma shinkafa, masara, dawa, gero, wake, waken suya, gyaɗa, barkono da sauransu, amma a lokacin damina ko kakarsu da ya kamata a same su da sauƙi sai a samu wasu azzaluman mutane su saye, su ɓoye, suna jiran ya yi tsada, su fito da shi su siyar su samu riba mai yawa, don kawai son zuciya da buƙatar kansu.
Kasuwanci ba Haram ba ne. Fita da kaya zuwa wasu ƙasashen, ba haram ba ne. Amma me zai sa gida bata koshi ba a kwashe a kai dawa? Duk ƙasar da suke fama da matsalar karyewar tattalin arzikin ƙasa ba sa fita da kayan abinci, don sauƙaƙa raɗaɗin wannan karyewar tattalin arzikin ƙasar tasu ga talakawan ƙasar.
Don haka ko da akwai laifin gwamnati wajen haifar da tsadar kayan masarufi a ƙasa sakamakon tashin Dala da kuma ƙarin haraji da janye tallafin man fetur, to, ’yan kasuwa da talakawa ma suna da masu laifin na saye kayan abincin suna fita da shi ƙasashen ƙetare ko Kudu, don su sayar da tsada su samu riba.
Uncle Larabi marubuci ne mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jihar Kano. Nigeria. Za a iya samun sa a 08065418892
