Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dikko Umar Raɗɗa ta yi kira ga al’umar jihar akan su tashi tsaye don su kare kansu daga hare haren ɓarayin daji waɗanda ke ci gaba da addabar wasu ƙananan hukumonin Jihar.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Dakta Nasir Mu’azu Ɗanmusa ne ya yi wannan kira lokacin da yake ganawa da manema labarai a babban birnin jihar.
Kwamishinan ya nuna damuwarsu game da yadda al’uma ke fargabar fito na fito da ‘yan ta’addan duk da cewa sun fi ‘yan bindigar yawan makamai.
A cewar Ɗanmusa, yan bindigar da ke addabar ƙaramar hukumar Batsari bindigogin da suke da su ba su wuce guda 34 ba, a yayin da al’umar ƙaramar hukumar ke da bindigogi aƙalla 800.
“A yankin Batsari kawai, akwai jami’an tsaro da jami’an tsaro na al’uma, akwai kuma ‘yan sa kai da ɗaiɗaikun mutane da ke da bindigogi”. Inji shi.
Kwamishinan ya ce, matsalar tsaro a jihar ta faru ne a dalilin harkokin noma wanda shine ke baiwa ‘yan ta’adda damar gudanar da harkokin su na ta’addanci.
Kazalika, cikin watan Fabrairu,2024 gwamnan jihar Dikko Umar Raɗɗa shima ya yi irin wannan kiran ga al’umar jihar a lokacin da ya jagoranci wani zaman tattaunawa tare da jami’an tsaro, jami’an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a harkar tsaron jihar.
A cewar gwamna Raɗɗa, bai kamata al’uma su naɗe hannu suna jiran sai gwamnati ta kare su daga hare haren ‘yan bindigar.
“Gwamnatin Jihar Katsina a shirye take don ta taimaki al’umar jihar da dukkan abunda suke buƙata don su kare yankunansu.” Inji gwamnan.
