Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF) a ranar Laraba ya koka kan yadda ake karkatar da kayan abinci mai gina jiki da aka tanada domin yara a wasu yankunan Jihar Sakkwato.
Shugaban ofishin UNICEF mai kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, Micheal Juma, ya bayyana damuwarsa a yayin taron masu tsara manufofi na kowace shekara a ranar Laraba a Sakkwato.
Juma ya buƙaci al’umma da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da su ƙara sanya ido kan yadda ake karkatar da kayayyakin abinci mai gina jiki na yara a jihar.
UNICEF ta shirya taron ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Sokoto domin tattauna batun ayyuka, nasarori, da ƙalubale da samar da hanyoyin magance ƙalubalen.
Juma, wanda Abraham Mahama ya wakilta, ya bayyana cewa, masu bayar da tallafi ne suka samar da kayayyakin abinci mai gina jiki, kuma an raba su ga cibiyoyin kiwon lafiya a al’ummomi daban-daban da nufin inganta rayuwar yara masu fama da tamowa.
Ya koka da cewa wasu mutane a cikin tsarin sun haɗa kai da ‘yan kasuwa tare da sayar kayayyaki.
Ya ƙara da cewa ana sayar da kayan a kasuwanni a bayyane.
A yayin bincike a shaguna, UNICEF ta gano cewa ma’aikatan sun canja wa kayan abincin kwalaye don rufe munanan ayyukansu.
Juma ya kuma buƙaci gwamnatin Sokoto da ta bi sahun sauran jihohin ƙasar wajen naɗa babban jami’in ƙididdiga wanda zai gaggauta tattara bayanai, adanawa da kai kayan bisa tsarin zamani.
