RA’AYI: Matsalar yunwa a Nijeriya: Ina mafita?

Spread the love

Daga HASSAN IMRAN

Assalamu Alaikum. ‘Yan uwana, yau na zo da wata taƙaitacciyar nasiha ne akan matsalar yunwa a ƙasar nan da nufin ba da shawarwari da samar mafita.

Matsalar yunwa ta zama ruwan dare a Nijeriya. Al’ummar ƙasa sun fara fuskantar tsananin fatara da tsadar rayuwa ne tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanar da janye tallafi man fetur wanda ya kasance ummul haba’isin hauhawar farashin abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar nan. Sanin kowa ne yunwa masifa ce babba wacce idan ta yaɗu takan kawo cututtuka da fitintinu a cikin ƙasa, wanda har ya kan iya shafar sha’anin tsaro. Haka za’alika takan haifar da mummunan tunani ga mutum ta kuma hargiza wa mutum rayuwarsa.

Sanin kowa ne cewa a halin da ake ciki yunwa ta sa talakawa a Nijeriya musamman a nan yankin Arewa sun shiga wani yanayi na tashin hankali. Yunwa ta ratsa mutane har kamar za ta halaka su. Sau da dama za ka ga mutum na tafiya yana surutai saboda ba ya cikin hayyacinsa. Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana yawan neman tsarin Ubangiji daga yunwa. An rawaito cewa daga cikin addu’arsa yana cewa, “Ya Ubangiji ina neman tsarin ka daga yunwa domin ita mummunan al’amari ne.”

A makon da ya gabata, jaridar Leadership Hausa ta rawaito wani mawuyacin halin da wasu talakawan jihohin Borno da Bauchi suke ciki. Mutanen yankin suna zuwa daji su tona gidan tururuwa don neman abinci. Abin tashin hankali shi ne mafi yawansu mata ne. Yunwa ta shigar da su wani yanayi. A wannan yanayi na rashin ingantaccen tsaro suna iya haɗuwa da wata muguwar dabbar daji da za ta iya cutar da su ko ta halaka su.

Tashin farashin kayan abinci ya jefa al’umma musamman talakawa a cikin galin tsaka mai wuya. A halin da muke ciki, mutane sun koma suna cin wasu nau’ikan abincin da basu saba da su ba suna sanya musu ciwo ko halaka su. A wasu yankunan na karkara mutane na zuwa daji su ɗebo ‘tafasa’ su kawo gida su dafa su hada shi da garin ƙuli-ƙuli su ci. Rashin samun wadataccen abinci mai gina jiki yana kawo cututtuka kamar cutar gyambon ciki da tamowa da sauransu.

Musabbabin wannan matsalar ta abinci ita ce saurin janye tallafi mai fetur da gwamnatin tarayya ta yi ba tare da saka wasu ƙwararan matakai a ƙasa ba, waɗanda za su kawo wa al’umma sauƙin rayuwa. Hakazalika, akwai wasu gurɓatattun ‘yan kasuwa da suke kai abincin ƙasashen ƙetare da ke kusa da mu domin sayar da su da niyyar samun riba mai yawa. Bugu da ƙari wasu ‘yan kasuwa sukan ɓoye kayan hatsi da sauran nau’ikan abinci domin idan sun yi ƙaranci su fito da shi su samu riba mai yawa. Haka kuma, rashin tsaro da ake fama da shi ya sa manoma da dama basa iya zuwa gonakinsu domin tsoron kar ‘yan ta’adda su yi musu illa ko kuwa su yi garkuwa da su.

Hanyoyin magance wannan matsalar sun haɗa da buƙatar gwamnati ta inganta tattalin arziƙin ƙasa, kuma ta kafa kwamitin kwararru da za su duba tsadar abinci don su rage raɗaɗin da al’umma ke ciki. Sa’annan ta ƙara duba yiwuwar dawo da tallafin man fetur. Haka kuma Gwamnatin ta sanya ƙwararan dokoki domin hana ‘yan kasuwa kai abincin wata ƙasa. Masu iya magana na cewa, ita sadaka daga gida ake farawa, sai ‘yan gida su wadatu kafin a kawai maƙwabta. Ya kamata masu hannu da shuni su taimaka wa talakawa da kayan abinci domin rage masu wahalhalun rayuwa. Gwamnatin Tarayya da al’umma su bai wa jami’an tsaro haɗin kai da samar musu da ingantattun bayanan sirri da za su taimaka musu wajen kama masu tada zaune tsaye. Yin haka, zai ƙarfafa gwiwar manoma domin su yi nomansu cikin natsuwa da kuma kwanciyar hankali. Haka kuwa, yin haka zai kawo sauyi wannan raɗaɗin tsadar rayuwa da al’umma ke ciki.

Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa, Ya kuma shige mana gaba. Amin.

*Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan lambar waya 09059323221

By ukarofi