
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar likitocin Nijeriya (NARD), ta umarci mambobinta su dawo bakin aiki bayan shafe mako guda ana yajin aikin gargaɗi.
An fara yajin aikin ne don nuna damuwa kan sace wata likita mai suna Dakta Ganiyat Popoola da aka yi watanni takwas da suka gabata.
Duka da cewa sun koma bakin aiki, ƙungiyar ta ce za su yi nazari kan ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen amsa buƙatunsu acikin makonni uku.
Dakta Popoola wata likita ce da ke aiki a Asibitin Ido na Ƙasa da ke Kaduna wacce aka yi garkuwa da ita tare da mijinta da wani ɗan wajenta a ranar 27 ga watan Disamba, 2023.
Daga bisani an sako mijin nata yayin da ita da ɗan suke hannun ƴan bindigar har zuwa yanzu.
A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta ce za ta zartar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’ ga likitocin.
Shugaban NARD, Dakta Dele Abdullahi ya ce sun dakatar da yajin aikin a halin yanzu, amma za su yi nazari kan ƙoƙarin gwamnati na tsawon makonni uku.
