Yadda Isra’ila ke cigaba da cin karenta ba babbaka a yaƙinta da Palestine

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Bayan shafe tsawon kwanaki 342 ƙasar Isra’ila na buɗe wuta wa makofciyarta ta Palastine, sojojin Isra’ila ƙarƙashin jagorancin shugabannin siyasa da na soji tare da taimakon Amurka, na cigaba da kisan kiyashi da rushe gine-gine da ɗaiɗaita al’ummar Palestine a wani yunƙuri na ramuwar gayya.

Cikin wata takarda da Jakadan Palestine, Abdullah Abu Shawesh ya fitar, ya ce haɗin-gwiwa tsakanin Isra’ila da Amurka akan mutanen Palestine na ɗaya daga cikin mummunan yanayi da aka taɓa shiga a tarihi kamar yadda ƙididdiga ta nuna.

Ya ce, ƙasashen da a duniya suke ikirarin sun fi kowa ƙoƙarin kare ƴancin ɗan-adam da gabatar da lakcoci akan tauye haƙƙin ɗan-adam da dokar ƙasa-da-ƙasa, yanzu kuma su ke karya waɗanda dokokin da ƙa’idojin ƴancin ɗan-adam.

Abu Shawesh ya ce, Amurka da Isra’ila suna aiki ne da dokar kama karya a fili ba tare jin nauyin hakan ba.

Ya ce, zuwa ranar 11 ga watan Satumba, 2024, adadin mace-mace ya kai 41,000 inda na waɗanda suka ji raunuka ya kai 95,000 yayin da 10,000 suka ɓata.

Bugu da ƙari, aƙalla ƴan Palestine 10,400 ne aka kama kuma aka yi garkuwa da su tun farkon yaƙin, waɗanda galibi ake azabtar da su tare da rashin ba su kulawa ta magani.

Game da makomar Ilimi kuma, ranar 9 ga watan tara ce ranar bai wa Ilimi Kariya daga Hari ta Duniya kuma ita ce ranar farko ta zangon karatu na 2024/2025 a Palestine. A Gaza, babban birnin ƙasar, sama da ɗalibai 630,000 ne suka rasa ƴancin zuwa makaranta da 58,000 da ba su samu shiga jami’o’i ba da kuma 39,000 da ba su rubuta jarrabawar manyan makarantu ba.

Aƙalla yaƙin ya yi sanadiyar mutuwa da raunata ɗalibai 25,000 wanda hakan ya kai ga ruguje kaso 90 na makarantun gwamnati.

Haka nan, daga ranar 1 zuwa 31 ga watan Agusta, 2024, tirela 69 na kayayyakin jin-ƙai ke shiga Gaza, saɓanin guda 500 da ake buƙata a kowacce rana.

By Babaji