Yayin da al’ummar Jihar Edo ke dakon sanar da sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar jiya, magogya bayan jam’iyyar PDP sun yi wata zanga-zanga ne a ofishin INEC da ke babban birnin ta Benin domin nuna rashin jin daɗin su kan yadda sakamakon zaɓen ya ke fita.
A sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta fitar daga ƙananan hukumomi 16 daga cikin 18, jam’iyyar APC ta samu nasara a ƙananan hukumomi 10 yayin da PDP tai nasara a shida. Wannan sakamakon ya janyo cece-kuce da ya sa magogya bayan PDP zagaye harabar su na ɗaga ganye suna waƙe.
Masu zanga-zangar na ikirarin an tafka maguɗi sosai a zaɓen domin alƙaluman da aka fitar a ƙananan hukumomi da dama ya bambanta da abinda INEC ke sanarwa.
Magogya bayan sun yi kira da shugaban ƙasa ya shiga lamarin domin gudun kar rikici ya ɓarke a jihar wajen sauyawa mutane abinda suka zaɓa.
