‘Yan wasan Nijeriya Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun koma Kano Pillars kan kwantiragin gajeren wa’adi na gasar firimiya ta Nijeriya na kakar 2024/25.
An dai ɗauki hoton ‘yan wasan biyu a filin atisayen Kano Pillars a ranar Alhamis gabanin wasan su na mako biyar na NPFL a gida da Sunshine Stars.
“Ahmed Musa, Shehu Abdullahi, Nazir Laja, da sauran ‘yan wasan sun yi atisayen tunkarar wasan NPFL 2024/25 Mako na biyar da Sunshine Stars a ƙarshen mako,” in ji ƙungiyar ta kafar sadarwar X ranar Juma’a.
Musa mai shekaru 31 a duniya ya koma Pillars karo na uku bayan ya buga mata wasa tsakanin 2009/10 zuwa 2021.
A ɗaya ɓangaren kuma Abdullahi zai buga wa Pillars wasa a kakar wasa ta bana, inda ya buga mata wasa a shekarar 2012.
Tun a watan Janairun 2023 ɗan wasan na tsakiya ya kasance ba shi da ƙungiya yayin da Musa kuma ya soke kwantiraginsa da kulob din Sivasspor na Turkiyya a watan Fabrairu.
Ko da yake an rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta NPFL 2024/25, yan wasan biyu sun sami damar shiga cikin tawagar a matsayin ‘yan wasa.
Shi ma shugaban gasar NPFL Sunday Obaseki ya tabbatar wa manema labarai haka a lokacin da Musa ya yi tsokaci game da komawar sa gasar ta Nijeriya.
“Eh, ana iya yi masu rajista. Don haka ba za su sami matsala ba, “in ji Obaseki.
