Dikko Raɗɗa ya raba Naira biliyan uku ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutane 1,067 da ambaliyar ruwan sama ya shafa a jihar Katsina suka amfana da tallafin kuɗi fiye da biliyan uku daga gwamnatin tarayya.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a wajan bikin bada taimakon kuɗi ga mutanen da ambaliyar ruwan sama ya shafa a Katsina.

Ya sanar da cewa mutum 1,067 kwamitin da gwamnati ta kafa ƙarƙashin mataimakin gwamna suka tantance.

Malam Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa mutum 439 da gidajen su suka rushe gaba ɗaya suka sami Naira 600.000,sai kuma waɗanda wasu sassan gidajen su ya rushe suka sami Naira 300.000.

Haka gwamnatin jihar ta sayi kayan gini na kimanin Naira miliyan 200 da ta rabawa mutum 1,773 waɗanda gidajen su gaba ɗaya ya rushe.

Yace ambaliyar ruwan ya kawo rushewar gidaje,rasa gonakai,lalacewar hanyoyi da wasu gine-gine na ma’aikatun gwamnati.

Gwamnan ya yabawa gwamntin Tinubu da hukumar jinƙai ta ƙasa da gudunmumar da suke ba hukumar bada agajin gaggawa a jihar.

Shugaban kwamitin tantance waɗanda ambaliyar ruwan ya shafa kuma mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe yace Naira miliyan 451 aka raba wa mutanan da iftala’in ambaliyar ruwan ya shafa.

By ukarofi