Gwamna Abba ya miƙa suneyen sababbin kwamishinoni ga Majalisar Dokokin Kano don tantancewa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika wa Majalisar Dokoki sunayen mutane shida da ya ke son naɗawa a matsayin kwamishinoni domin neman amincewa.

A makon da ya gabata ne gwamnan ya yi wa Majalisar Zartarwarsa garambawul tare da sallamar wasu daga cikin mambobinta.

Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Ismail Falgore ya karanta takardar saƙon a yayin zaman majalisar na ranar Litinin.

Waɗanda aka miƙa sunayen nasu sun haɗa da; Alh. Shehu Wada Sagagi, Alh. Abdulkadir Abdulsalam AG, Ibrahim A. Waiya, da Dakta Isma’il Ɗanmaraya da Dakta Ghaddafi Sani Shehu da kuma Dakta Dahir M. Hashim.

Kazalika, majalissar ta buƙace su da su bayyana a gabanta a ranar Talata da misalin karfe 10 na safe domin tantance su.

Ga dai sunayen ma’aikatun da a yanzu haka ba su da kwamishinoni: Ma’aikatar raya karkara da Ma’aikatar kuɗi da Ma’aikatar Muhalli da Ma’aikatar yaɗa labari da Ma’aikatar Makamashi da kuma Ma’aikatar Jin-ƙai.

By Babaji