Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Sabon Shugaban ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa, Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya yaba wa sabon babban sakatarensa na ƙaramar hukumar Mista Abraham Ekpo dangane da aiki tuƙuru da kuma ƙwarewarsa a aikin na sakatare.
Shugaban ƙaramar hukumar Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a sakatariyar ƙaramar hukumar dake Karu ranar Laraba na mako da ake ciki.
Ya ce tabbas da shi da sauran shugabannin ƙaramar hukumar ba su yi zaɓin duhun dare ba na zaƙulo Mista Abraham Ekpo tare da na da shi babban muƙamin na sakataren ƙaramar hukumar a ‘yan kwanakin baya idan akayi la’akari da gagarumin gudumawa da sadaukarwa da mista Abraham Ekpo ke cigaba da bayar wajen inganta tare da bunƙasa harkokin gwamnatin ƙaramar hukumar ta Karu kawo yanzu.
Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya ce duk da cewa kafin ya zaɓi ya kuma na da Mista Abraham Ekpo a matsayin babban sakataren ƙaramar hukumar yasan ba zai yi nadaman yin haka ba amma a yanzu haka Abraham yana cigaba da ba shi mamaki ta ƙwarewar sa sosai a aikin.
Ya cigaba da bayyana cewa “A gaskiya ina so in yi amfani da damar nan in sanar da kai cewa mukan a ƙaramar hukumar nan ta Karu mun yi dacen sakatare wato Mista Abraham Ekpo kasancewa tunda ya kama aiki a wannan muƙamin sa tabbas yana bada gagarumin gudumawa kuma a matsayi nan a shugaba ina matuƙar alfa’ari da shi sosai don a yanzu samun irin sa yada da matuƙar wahala.
Mista Abraham Ekpo ina tabbatar maka cewa mutuum ne dake sadaukar da komai tare da yin aiki tuƙuru ga kuma uwa uba nuna gaskiya da adalci wajen bai da nasa gudumawa a ƙoƙari da muke yi tare wajen kawo canje-canje masu ma’ana a ƙaramar hukumar nan ta Karu dama jiha baki ɗaya.
Don kamar yadda ka sani a ‘yan kwanakin nan ne a matsayina na shugaban ƙaramar hukumar nan na nada shi a matsayin babban sakatare duk da bai daɗe a kujerar ba amma gaskiya kawo yanzu mun gano cewa ƙwarerre ne mai kuma kishin cigaban ƙaramar hukumar baki ɗaya.? Inji shi.
Dangane da shirye-shirye na musamman da gwamnatinsa a ƙaramar hukumar ke shirin aiwatar don cigaban yankin a sabuwar shekarar nan ta 2025 shugaban wanda aka zaɓe shi kwanakin baya a shekarar daya wuce 2024 Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya bayyana cewa a yanzu aka akwai ingantattun shirye-shirye na musmman da gwamnatin sa zata cigaba da aiwatar kamar yadda ta faro da suka haɗa da samar da tsaftaceccen ruwan sha da gyara hanyoyi da samar wa karamar hukumar kuɗaɗen shiga da tabbatar da tsaro a yankunan baki ɗaya da kiwon lafiya da dai sauran su inda ya bukaci al’ummar karamar hukumar baki daya su cigaba da basu cikakken goyon baya don cimma muradun a sabuwar shekarar.
Idan ba a manta a shekarar daya gabata 2024 ne aka zabi sabon shugaban karamar hukumar ta Karu honorabul barista Abubakar Aliyu Madaki inda shi kuma nantake ya nada tare da rantsar da mista Abraham Akpo a matsayin babban sakataren karamar hukumar.
