Gwamnatin Katsina ta ɗauki mutane 34,000 aiki a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A cikin shekara biyunta na farko, gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki mutane 34,000 aiki a fannoni daban-daban a faɗin jihar.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a wajen bikin bada tallafin kuɗi ga mata 600 domin inganta kiwo a ƙarƙashin Gidauniyar Kabir Magaji Gafiya a garin Kaita.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Malam Farouk Lawal Joɓe, ya ce babu wata gwamnati a ƙasar nan da ta ɗauki adadin waɗannan mutane aiki.

Hakan ya nuna ƙoƙarin gwamnatin Raɗɗa na rage adadin rashin aikin yi da kuma inganta rayukan al’ummar jihar, acewar mataimakin.

Ya kuma ce, acikin waɗanda aka ɗauka aiki akwai ta fanin addini, inda ake bai wa limamai da ladanan masallatan Juma’a alawus a kowane wata.

Joɓe ya ce, a lokacin da suka karɓi mulki a jihar, sun yi nasarar naɗa ma’aikata 22,000 da SUBEB suna da ma’aikata 25.

Ya kuma bayyana mahimmancin zuba jari akan harkar noma da kiwo wanda akan hake gwamnatin ta ke a halin yanzu.

By Babaji