Ba za mu tsawaita wa’adin rufe rijistar UTME ta bana ba – JAMB

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta ce wa’adin rajistar jarrabawar 2025 (UTME) da aka fara a ranar 3 ga watan Fabrairu yana nan daram ba za a tsawaita ba a ranar 8 ga watan Maris, 2025.

Kakakin hukumar ta JAMB, Dakta Fabian Benjamin, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce an bayyana wa’adin ƙarara sanarwa da tallace-tallace da kuma kalandar jarrabawar UTME ta 2025.

“Muna son sanar da duk masu zana jarrabawa cewa ba za a ƙara wa’adin rajistar ba. Wannan sanarwar na da muhimmanci musamman idan aka yi la’akari da raguwar adadin masu rajistar jarrabawar kwanan nan. 

“Muna kira ga duk waɗanda ke son shiga da su yi rajista cikin gaggawa kuma su guji jira har sai  zuwa ƙarshen lokacin,” inji shi.

By ukarofi