Haɗewar layin wutar lantarki ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mutane huɗu suka mutu wasu takwas suka sami munanan raunuka sakamakon haɗewar layin wutan lantarki a kwanan Ɗorawa da ke Sabuwar Unguwa cikin garin Katsina.

Haɗewar layin wutan lantarki ya janyo afkuwar mummunar gobara a unguwar.

Mubarak mazaunin unguwar ya ce mata uku da namiji ɗaya suka mutu,a cikin matan akwai Hassana,Murja da Halima.

Ya bayyana cewa akwai mutane takwas da suka sami raunuka musu muni daban daban da yanzu haka wasu na kwance a asibitin gwamnatin tarayya a Katsina.

Ya ƙara da an sami asarar ɗimbin dukiya da sai nan gaba za a tabbatar da adadin asarar da a kayi.

Sani Ibrahim mijin Halima ya shaidawa manema labarai cewa ya kaɗu ƙwarai da yaji labarin mai ɗakin sa Halima ta kama da wuta da a lokacin yana ce yana ƙoƙarin kashe firjin gidan,”anyi ƙoƙarin bata ruwa madara amma bata kai ga sha ba ta rasu.

Babu wani bayani daga kamfanin rarraba wutan lantarki KEDCO da na samar da wutan lantarki TCN da reshen ofisoshin su a Katsina.

By ukarofi