
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ikirarin cewa babu wata ƙaramar hukuma a jihar da za a sake bari ta faɗa hannun mayaƙan Boko Haram ko ISWAP duk da sake farfaďowar barazanar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas.
Zulum ya faɗi hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai jim-kaďan bayan zama da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.
Ya bayyana cewa, duba da haďin-gwiwa da ake samu a tsakanin sojoji da hukumomin al’umma da ƙauyuka a jihar, hakan zai taimaka wajen magance ayyukan mayaƙan.
“In Allah ya yarda da taimakon sojojin Nijeriya da taimakon jami’an tsaro, ba za mu bar ko ƙaramar hukuma ɗaya ta shiga hannun ƴan ta’addar ba.”
Musamman Zulum ya je wajen Shugaba Tinubu da nufin ba shi ba’asi kan taɓarɓarewar tsaro a yankin Arewa maso Gabas musamman a Borno da kuma neman faɗaɗa agajin Gwamnatin Tarayya.
A kwanan nan ne Zulum ya ziyarci ƙananan hukumomin da ke fama da matsalolin ta’addanci, inda ya yi nazari game da matakin matsalolin acikinsu musamman wajen ɗaiɗaita sansanonin sojoji.
Kazalika, ya yaba wa Gwmanatin Tarayya bisa matakan da ta ɗauka wajen magance matsalolin, inda ya ce suna sa rana nan ba da jimawa ba za su haifar da kyawawan sakamako .
