Gini ya rufta wa ɗalibai suna tsaka da rubuta jarrabawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Daruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE) suka rufta a ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba.

Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska.

ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su.

Wani mazaunin garin Alhaji Dan Azumi Lauris ya shaida manema labarai cewa, ajujuwan sun ruguje karo na biyu da ɗalibai, lokacin da rukunin farko ya gama jarrabawa ya bar harabar makarantar.

Ya ce, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin Laraba.

Dan Azumi, ya bayyana cewa, an kai ɗalibai da malaman da suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke kusa da makarantar inda yanzu haka suke samun kulawa.

Ya ce, baya ga makarantar, guguwar ta lalata gidaje da dama a cikin unguwar.

By ukarofi