Gwamnatin Nijeriya za ta hukunta kamfanonin jiragen da ke shigo da baƙi ba biza

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi gargaɗin cewa, jiragen da ke jigilar fasinjoji ba tare da ingantacciyar biza zuwa Nijeriya ba, za a hukunta su.

Tunji-Ojo ya yi wannan gargaɗin ne a wani shiri na wayar da kan masu ruwa da tsaki kan aiwatar da shirin na ‘e-bisa’, ranar Juma’a a Legas.

A cewar ministan, ba za a bar wani ɗan ƙasar waje ya shiga Nijeriya ba tare da ingantacciyar biza ba.

Ya ce, duk da cewa Nijeriya na ƙara samun hanyoyin masu sauƙi na shiga ƙasar tare da ɓullo da sabon tsarin biza, hakan ba zai kawo cikas ga tsaron ƙasa ba.

Ya buƙaci Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nujeriya, NCAA, da ta tabbatar da cewa kamfanonin jiragen sama za su bi ƙa’idar biza ta Nijeriya ta 2025.

Tunji-Ojo ya ce tsarin e-Biza zai inganta tsaro a kan iyaka da kuma bunƙasa yawon shaƙatawa da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

“Ina roƙon hukumar ta NCAA da ta daidaita, don haka wannan taron wani shiri ne na haɗin gwiwa na ma’aikatar, Hukumar Kula da Shige da Fice ta ƙasa (NIS) da kuma NCAA.

“Ga kamfanonin jiragen sama, na san kuna nan don yin kasuwanci, amma kuma kuna da wani nauyi da ya rataya a wuyanku ta fuskar sha’anin ƙasa da kuma tsaro.

“Kafin kowa ya shigo Nijeriya, don Allah a duba bizarsa, ba wai kawai shaidar biyansa ko tikitin sa kaɗai za a duba ba.

“Ba a yarda da shi a cikin Burtaniya, Amurka, Kanada da sauran ƙasashe ba, kuma ba za a amince da shi ba a Nijeriya kuma,” inji shi.

Ministan ya ce, samar da takardar neman biza ta e-ɓisa da katin sauka da na fita cikin sauƙi ya zama dole domin buɗe iyakokin Nijeriya ga masu zuba jari.

Ya bayyana cewa kamar yadda a ranar 22 ga Mayu, NIS ta karɓi jimillar masu neman biza ta e-Biza 5,814, ta amince da 5,671, ta ƙi 66 kuma ta nemi 62, tun lokacin gabatar da tsarin a ranar 1 ga Mayu.

By ukarofi