Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata kotun hukunta laifuka ta musamman da ke zamanta a jihar Legas da ke Ikeja ta samu Mamman Nasir Ali, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Ahmadu Ali, da ɗan Saliyo Christian Taylor da laifi, inda ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bisa laifin zamba na Naira Biliyan 2.2 na tallafin man fetur.
Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke wa mutanen biyu hukuncin ne tare da wani kamfanin mai, Nass Man Oil Serɓices Limited bayan kotu ta same su da laifin tuhume-tuhume 57 da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin aasa zagon ƙasa (EFCC) ta ke musu.
An fara gurfanar da wɗdanda ake tuhumar ne a gaban kotu a shekarar 2012 kan tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da haɗa baki wajen karɓar kuɗi ta hanyar ƙarya da kuma amfani da takardun bogi.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta yi ikirarin cewa laifukan sun saɓawa dokar damfara da sauran laifukan da suka shafi zamba ta shekarar 2006 da kuma dokar laifuka ta jihar Legas ta 2011.
Ta bakin mai shigar da ƙara, Seidu Atteh, EFCC ta kuma zargi waɗanda ake tuhuma da laifin damfara daga gwamnatin tarayya a ƙarƙashin shirin tallafin man fetur a ranar 9 ga Satumba, 2011.
Hukumar da ke Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta shaida wa kotun cewa waɗanda aka yanke wa hukuncin sun gabatar da takardun jabu, ciki har da na jabun rahoton “Gasoline Analysis” na MT Overseas Limar, wanda kamfanin Saybolt Concremat ya bayar.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Dada ta ce ta samu hujjojin da masu gabatar da ƙara suka gabatar mata da ƙarfi.
Ta yanke hukuncin cewa abin da masu laifin suka aikata ba kawai damfarar gwamnati ba ne, har ma tare da lalata amincin shirin tallafin man fetur na Nujeriya.
Baya ga zaman gidan yari, kotun ta kuma bayar da umarnin a kwace wasu kadarorin da aka gano da kuma asusun na banki da ke da alaƙa da badaƙalar.
Alƙalin ta kuma bayar da sammacin kama wasu mutane biyu, Oluwaseun Ogunbambo da Olabisi Abdul Afeez, waɗanda aka ce har yanzu suna ’yar ɓoya da jami’an tsaro.
