’
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa masu ra’ayin son kai na shirin durƙusar da Jihar Zamfara domin cimma muradun siyasar su, yana mai cewa ba za a amince da kafa dokar ta-ɓaci a Zamfara ba.
Dr. Shinkafi a wata zantawa da manema labarai a daren ranar Alhamis a Gusau, ya ce kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya a bayyane yake, waɗanda idanuwan su suke a rufe sun Kasa fahimtar me ya ƙunsa.
“Jihar Zamfara sam bata cancanci a ayyana dokar ta-ɓaci ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, ya kamata masu ɗaukar nauyin wannan tada zaune tsaye su yi nazari a kan abin da kundin tsarin mulkin ya ƙunsa, su fahimce shi da kyau kafin su yi munanan kalamai”. Ya bayyana.
A cewar sa, sashe na 305 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima, yana magana ne kan ayyana dokar ta ɓaci musamman ma, ya zayyana sharuɗɗan da shugaban ƙasa zai bi Kafin ya ayyana dokar ta ɓaci da kuma hanyoyin da ya kamata a bi.
“A ɗauki misali da Borno inda aka kashe dubbai, wasu sun rabu da muhallansu, Jihohin Benuwai, Taraba, Neja da sauran jihohin da ake fama da rashin tsaro amma me yasa a Zamfara ne kawai a keta kwakwazon ayyana dokar ta ɓaci”.
Dokta Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa na son kawo taɓarɓarewar zaman lafiya a jihar ta Zamfara.
Yayi zargin cewa masu ɗaukar nauyin tada zaune tsaye a jihar ne suka ɗauki nauyin ‘yan gudun hijira domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da rashin tsaro a jihar, inda yace Gwamna Dauda Lawal na yanzu ya gaji matsalar ce daga gwamnatin da ta shuɗe a jihar.
“Kira da kafa dokar ta-ɓaci a Zamfara aiki ne na ‘yan siyasa da su kayi gudun hijira daga jihar, suna son su durƙusar da jihar ne don biyan buƙatun su a siyasance”. Ya faɗa.
Ya kuma yi zargin cewa akwai maƙiya a ciki, waɗanda ke taimakawa tare da daƙile ayyukan ‘yan bindiga, ya kuma shawarci jami’an tsaro a jihar dasu sanya ido a kansu.
Dr. Shinkafi ya kuma nuna rashin amincewa da kalaman shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe a kwanakin baya wanda ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa a Arewacin ƙasar.
“Har yanzu mutane suna ƙangin yunwa, babu abinci, talauci, rashin tsaro, har ta kai ga mutane ba za su iya zuwa gonakin suba”. Inji Dr. Shinkafi
Ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin na ƙashin kansa, bada yawun alummar Arewacin Nigeria ba.
