Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sayo jiragen yaƙi 60 domin ƙara wa rundunonin tsaro ƙarfi wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a Nijeriya.
Air Marshal Abubakar ya bayyana hakan ne a wajen taron Sir Ahmadu Bello Foundation da ya gudana a Arewa House a Kaduna.
A cewarsa, wannan yunƙuri na daga cikin muhimman sauye-sauye da gwamnatin ke yi don tabbatar da zaman lafiya da kuma murƙushe ‘yan ta’adda a sassan ƙasar.
“Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba mu cikakken goyon baya. Za mu yi amfani da sabbin jiragen yaƙi wajen kai farmaki a duk inda barazana ke fitowa. Wannan wani sabon babi ne a ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali a Nijeriya,” inji Air Marshal Abubakar.
