Idan ban aure ki ba jini zai kwarara, inji matashin da ya kashe budurwarsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahotanni sun bayyana cewa, a daren ranar Larabar da ta gabata ne wata matashiya mai zane, kuma wadda ba ta daɗe da kammala NYSC ba, mai suna Deborah Moses, wadda aka fi sani da Deb’rah Porsche, aka same ta cikin tafkin jini a gidanta bayan wani tsohon saurayinta ya kashe ta.

Wanda ake zargin mai suna Linteɗ ɗan asalin garin Otukpo a jihar Binuwai, an yi zargin cewa ya  yi basaja a matsayin mai kai saƙo domin shiga gidan da Deborah ke zaune.

Lokacin da jami’an tsaron gidaje suka tayar da shi saboda shakku, an ce ya haye ta katanga ya shige gidanta.

A cewar shaidu, Linteɗ ya fara yin yunƙurin haifar da fashewa wani abu ta hanyar lalata bututun iskar gas ɗin Deborah Moses a wajen gidanta.

A lokacin da hakan bai samu ba, ya kutsa cikin gidanta tare da daɓa mata wuƙa sau da yawa, wanda hakan ya sa ta rasa ranta.

Majiyar dangin ta ce, Deborah Moses ta kawo karshen dangantakar ta da Linteɗ tun shekara guda da ta wuce amma ta ci gaba da fuskantar barazana daga wanda ake zargin.

“Ya kasance yana cewa, ‘Idan ban same ki ba, ba wanda zai same ki. Idan ban aure ki ba, jini zai kwarara,” inji wani dangin ta.

Deborah, wacce ta kammala NYSC kuma a hankali tana gina sana’arta, rahotanni sun ce tana guje wa kiran da ba a so da kuma ci gaba daga gare shi kafin rasuwar ta.

Makwabtan sun samu galaba a kan wanda ake zargin bayan harin inda suka miƙa shi ga ‘yan sanda. Yanzu haka yana tsare.

A halin da ake ciki dai, masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama da ‘yan uwa na neman a gudanar da cikakken bincike, inda suka dage cewa dole ne a tabbatar da adalci, kuma ba za a share shari’ar a ƙarƙashin kafet ba.

By ukarofi