Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hamshaƙin ɗan kasuwan Nijeriya, Femi Otedola, ya yi zargin cewa an karkatar da kuɗi har Naira Tiriliyan 2 a wani batun tallafin man fetur a ƙarƙashin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Otedola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya goyi bayan kamfanin man Dangote (DPR) a rikicin da take yi da ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (DAPPMAN).
A ranar 16 ga watan Satumba, DAPPMAN ta zargi matatar da aikata wasu abubuwa da za su kawo cikas ga kasuwa, inda ta yi iƙirarin cewa rage farashin man fetur da kamfanin ya yi, an tsara shi ne don raunana kasuwa maimakon biyan buƙatun ’yan ƙasa.
Otedola ya taya Dangote murna kan nasarar kafa matatar mai. Ya bayyana ta a matsayin babbar nasara ga ‘yancin Nujeriya a fannin makamashi da makomar tattalin arziki.
Otedola ya kuma yaba da matakin Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya kawo sabuwar damar samun sauƙi.
Otedola, wanda shi ne ya kafa DAPPMAN a 2002, ya soki ƙungiyar bisa rashin sabunta tsarin kasuwancinta, yana cewa lokaci ya wuce na dogaro da tallafin mai don shigo da kaya.
Ya bayyana cewa a baya, kafa rumbunan ajiya na man fetur na da amfani saboda tsarin shigo da mai ya kasance mara inganci.
Amma a cewarsa tun da yanzu Nijeriya na da matatar mai mai aiki da kyau, kamar ta Dangote, tsarin na baya ya zama tsohon tarihi.
Ya ce, “Na ba wasu daga cikin ‘yan DAPPMAN shawara a bara da su sayar da rumbunansu, domin yanzu yawancinsu ba su da amfani.”
A cewarsa, DAPPMAN tana neman Dangote ya biya tiriliyan N1.5 don raba mansa ga kwastomomi, amma ya ce hakan ba zai yiwu ba.
Ya jaddada cewa lokaci ya yi da ƙungiyar ta koma mayar da hankali kan tashoshin saida mai kai tsaye, ba wai rumbunan da ba sa aiki ba. A cewar Otedole, “Matatar Dangote ba matsala ba ce, ita ce mafita.”
Ya buƙaci su zuba jari a sababbin hanyoyi ko su haɗa kai su sayi matatar Fatakwai idan suna da kwarin gwiwar za su iya fafatawa a kasuwar mai.
“A game da tallafin, ni da kaina na gargaɗi Goodluck Jonathan cewa ana yaudararsa, an gina tsarin ne domin amfanar masu gidajen man, kuma ‘yan ƙungiyar DAPPMAN ne suka fara cin gajiyar shirin,” inji shi.
“Sama da Naira Tiriliyan 2 an ƙarƙatar da su ta hanyar zarge-zargen da ake tantama, dukkansu suna da alaƙa da lasisin ajiya. Manufar ba ta nuna gaskiya ko ƙirƙire-ƙirƙire ba, ta ƙarfafa neman hayar rashawa.”
Da yake magana kan abin da ya bayyana a matsayin “tatsuniya da ake ci gaba da maimaitawa”, Otedola ya ce raba man Dangote ba zai raba kowa da aikinsa ba kamar yadda wasu ke iƙirari.
