Majalisar Ƙasa ta amince da naɗin Farfesa Ojo Amupitan a matsayin sabon Shugaban INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Ƙasa ta amince da naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.

Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Amupitan a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci hukumar daga shekarar 2015 zuwa Oktoban 2025.

Tinubu ya shaida wa majalisar cewa farfesan, wanda asalinsa mutumin jihar Kogi a Arewa ta Tsakiya ne, ba ɗan siyasa ba ne, lamarin da ya ƙarfafa wa mambobin majalisar wajen amincewa da shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Gwamnan Kogi, Usman Ododo ya bada kyakkyawar shaida akan Amupitan da cewa mutum ne tsayayye akan harkokin da ya sa a gaba don haka zaɓar sa a matsayin shugaban INEC gagarumar nasara ce.

Za a miƙa sunan Farfesan zuwa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma tabbatar da shi a muƙamin shugaban hukumar zaɓen bayan kammala aiki akan lamarin.

Amupitan mai shekaru 58 ɗan garin Ayetoro Gbede ne da ke Ƙaramar Hukumar Ijumu a Jihar Kogi, sannan Farfesan Shari’a ne a Jami’ar Jos (UniJos) ta Jihar Filato kuma tsohon ɗalibin jami’ar ne.

Sannan, tun a watan Satumban 2014 ne Amupitan ya zaman babban lauyan Nijeriya, wato SAN.

A wata takarda da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an haifi Farfesan ne a ranar 25 ga watan Afrilu, 1967.

Bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare, ya halarci makarantar Polytechnic ta jihar Kwara da ke Ilorin daga 1982 zuwa 1984 sai kuma Jami’ar Jos daga 1984 zuwa 1987. A shekarar 1988 kuma ya zama lauya.

By Babaji