Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dandalin Shugabannin Matasan Arewacin Nijeriya (NNYLF) ta gargaɗi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Omoyele Sowore, da su daina tsoma baki cikin lamarin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda yake tsare.
Matasan sun ce ba za su zauna su yi shiru ba su bar Atiku da Sowore su yi amfani da batun Kanu a matsayin kayan siyasa don tayar da hankalin ƙasa ba. Sun nemi su bar kotu ta ci gaba da sauraren shari’ar da ta shafi tuhume-tuhumen ta’addanci da ake masa.
Shugaban ƙungiyar, Comrade Murtala Muhammed Gamji, ya bayyana wannan matsayi ne a taron manema labarai da suka gudanar a Abuja a ranar Talata, inda suka kuma sanar da shirinsu na gudanar da zanga-zangar goyon baya ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu daga ranar 20 ga Oktoba, 2025.
A baya-bayan nan ne Atiku Abubakar ya goyi bayan kira da Sowore ya yi ga gwamnatin tarayya da ta saki Nnamdi Kanu, yana mai cewa ci gaba da tsare shi “tarnaƙi ne ga doka da adalci a Nijeriya.”
Kanu dai yana fuskantar tuhumar ta’addanci, cin amanar ƙƙasa, da tayar da fitina a kotun tarayya da ke Abuja, duk da cewa kotuna da dama sun taba bayar da umarnin a sake shi.
Atiku, wanda ya taba zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, ya wallafa a shafinsa na ɗ cewa, “Ci gaba da tsare Mazi Nnamdi Kanu abin kunya ne ga ƙasar nan da kuma tabo ga imaninmu ga mulkin doka. Rashin bin umarnin kotu cin zarafi ne ga adalci. Ina goyon bayan kira da Sowore ya yi don a saki shi nan take ko kuma a gurfanar da shi cikin gaskiya.”
Sowore kuwa ya bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar neman a saki Kanu ranar 20 ga Oktoba, 2025, inda ya gayyaci gwamnoni, sanatoci, da fitattun shugabannin yankin Kudu maso Gabas, ciki har da Peter Obi, su shiga wannan gangami.
Sai dai a nasa martanin, Kwamaret Gamji ya ce, “Muna nan don mu nuna fushinmu da rashin amincewarmu da wasu ’yan siyasa masu neman amfani da sunan Nnamdi Kanu don tada hankalin ƙasa. Atiku Abubakar da Sowore suna shirya zanga-zanga, amma mu muna cewa a’a. Kada ku yi amfani da jinin matasan Nijeriya don cimma burinku na siyasa.”
Ya ƙara da cewa, “Ranar da za su fito, ita ce ranar da matasan Arewa sama da miliyan 63 za su mamaye titunan Abuja don nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ayyukan da yake yi.”
ƙungiyar ta ce, zanga-zangar goyon bayansu za ta gudana daga ranar 20 zuwa 23 ga Oktoba, domin nuna cikakken goyon baya ga shugabancin Tinubu da manufofin gyare-gyare na gwamnatinsa.
