Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙoƙarin da ya ke yi domin inganta harkar lafiya, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya ƙaddamar da aikin gyaran Asibitin Ƙofar Durbi Kwanar Yan Lemo da ke cikin mazaɓar Wakilin Gabas 1 cikin garin Katsina.
Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar, Hon. Miqdad ya bayyana cewa aikin zai gudana ne cikin matakai biyu domin tabbatar da cikakken gyara mai ɗorewa da inganci.
Ya ce a Kashi na farko, aikin zai haɗa da gina katangar zagaye, cikakken gyaran gine-ginen da suka lalace, tare da samar da muhimman kayan aikin asibiti da za su taimaka wajen inganta kula da lafiya da tabbatar da tsaro da walwalar marasa lafiya da ma’aikata a asibitin.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa a Kashi na biyu, wanda za a fara nan da wata mai zuwa, za a gina sabon ɗaki na musamman da zai iya karɓar marasa lafiya har mutum goma (10) a lokaci guda. Ya ce wannan matakin zai magance matsalar ƙarancin ɗakunan kwana da asibitin ke fama da ita, wanda a halin yanzu mara lafiya ɗaya kacal yake iya kwana.
Shi ma Injiniya Muhammad Hassan, da ke jagorantar aikin gyaran asibitin, ya tabbatar wa shugaban ƙaramar hukumar da al’ummar yankin cewa za su kammala aikin akan lokaci da gudanar da aiki mai inganci da nagarta.
Ya bayyana cewa kamfanin su zai tabbatar da cewa asibitin da za a miƙa bayan kammala aikin zai kasance mai ɗorewa kuma ya dace da ƙa’idodin aikin lafiya.
A nasa jawabin, Hon. Zaharaddeen Sirajo, Kansila mai wakiltar mazaɓar Wakilin Gabas 1, ya nuna godiya ga shugaban ƙaramar hukumar bisa amsa kira cikin gaggawa da kuma jajircewarsa wajen ganin an farfaɗo da aikin gyaran asibitin.
Kabilar ya ce an yi ta neman yadda za a yi wannan gyara tun zamanin gwamnatocin da su ka wuce, amma ba a sami nasara ba sai a lokacin jagorancin Hon. Miqdad, wanda bayan ziyarar gani da ido, ya ɗauki mataki kai tsaye don ceto asibitin.
Taron ƙaddamarwar ya samu halartar nataimakin shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Usman Yusuf Saulawa, sakataren ƙaramar hukuma, Hon. Abdulkarim Modibbo, sauran kansiloli, sakatariyar Ilimi ta Katsina LGEA, Dr. Halima Umar Kofar Sauri, da fitattun dattawan al’umma irin su Alhaji Dikko Bala, shugaban majalisar dattawan Gabas 1, da Alhaji Abdulrahman Marafa, da sauransu.
