Dan uwa ya cire wa ƙanwarsa idanu don neman kuɗi a Bauchi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Bauchi ta kama mutum shida da ake zargi da hannu cikin mummunan laifin cire wa wata yarinya mai shekaru bakwai idanu don yin asiri da nufin neman kuɗi.

ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Auwalu Muhammad, shi ne aka bayyana cewa ya kai ƙanwarsa, Rukayya Muhammad, cikin daji da ke Bayan Dutse a yankin Wailo, ƙaramar hukumar Ganjuwa, inda ya kai mata hari ya cire mata idanu biyu.

Rahoton rundunar ya ce, an ceto yarinyar, aka garzaya da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Sir Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda take ci gaba da karɓar magani.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa binciken farko ya nuna cewa Rukayya ta rasa gani da idanuwanta har abada sakamakon wannan ɗanyen aiki.

“Wata ’yar shekara bakwai mai suna Rukayya Muhammad ta rasa idanuwanta gaba ɗaya bayan ɗan uwanta, Auwalu Muhammad, ya cire su domin yin asiri da nufin samun dukiya,” inji Wakil.

Ya ƙara da cewa, sauran mutanen da aka kama su ne Mohammed Rabiu, Saleh Ibrahim, Nasiru Muhammad, Hassan Garba, da Garba Dahiru — kuma duk sun amsa laifin a yayin tambaya.

Wakil ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano cikakken dalilin da ya sa suka aikata wannan ta’asa, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin zai fuskanci hukunci.

By ukarofi