Ku yi amfani da alƙalumanku wajen gina ƙasa ba rusawa ba – Tinubu ga editoci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Laraba Shugaba Bola Tinubu ya kirayi editocin Nijeriya da su cigaba da tsare gaskiya da adalci yayin fitar da rahotanni, yana mai roƙon su da su riƙa amfani da ofisoshinsu wajen ƙoƙarin inganta harkar dimukraɗiyya da haɗin kan ƴan ƙasa.

Da yake jawabi yayin buɗe babban taron Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) na shekara-shekara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya ce fannin jarida sh ine ƙashin bayan ci-gaban ƙasa da ƙarfafa shugabancin dimukraɗiyya a sassan ƙasar.

Taron ya haɗa jagororin jaridu, manyan ƴan jarida, masu samar tsare-tsare da malaman harkar sadawar daga sassa daban-daban na faɗin Nijeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba da ƙoƙarin harkar jarida a Nijeriya bisa yadda suke taimaka wa bunƙasar harkar siyasar ƙasar, inda ya bayyana aikin jarida a matsayin abinda ke ƙarfafa ƙasa da ke bada kariya ga ƴanci, adalci da gaskiya.

Ya ce, da dama daga cikin ƴan jarida sun fuskanci cin fuska, tsarewa da wasu matsalolin rayuwa da takura duk domin maslahar al’umma a sakamakon sadaukarwarsu, yana mai cewa hakan ya sa suak cancanci yabo da jinjina.

Ya ƙara da cewa, editoci da manajojin gidajen jaridu, suna da rawar ganin cewa an inganta saƙonnin da ake yaɗa wa al’umma da wayar da kan ƴan ƙasa.

By Babaji