
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jinjina wa ƴan ƙabilar Igbo, inda ya bayyana su a matsayin waɗanda suka fi tasiri a harkokin al’amuran ƙasa da kasuwanci.
Shettima ya faɗi haka ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin taron masu ruwa da tsaki na tattali na Imo da aka gudanar a birnin Owerri.
Ya ce, Inyamurai mutane ne da ke ƙoƙarin kutsa kai a kowane ɓangare na ƙasa don gudanar da harkokin kasuwanci da naman ilimi.
Shettima ya bayyana cewa, ƴan ƙabilar sun taimaka wajen bada gagarumar gudumawa ga ci-gaban ƙasa don haka ya zama wajibi gwamnati ta tallafa musu da kayan aiki wajen cimma kyawawan manufofinsu na ciyar da tattalin arziƙin ƙasa gaba.
Ya cigaba da cewa a zamanin yau duniya ta daina dogaro da tattalin albarkatun ƙasa kaɗai sakamakon samun ci-gaba ta fuskar fasaha da ƙirƙira, wanda a yanzu su ne ƙashin bayan ci-gaba.
Da yake jawabi, Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo ya yaba wa tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu, wanda acewarsa sun taimaka wajen samar da yanayi mai kyau ga masu son zuba jari a harkokin ƙasar.
Ya bayyana cewa, tuni jiharsa ta fara ƙoƙarin bin tsare-tsaren Shugaban Ƙasar da nufin yin fintinkau wajen ci-gaban shiyya.
