Tirela ta murƙushe ɗaliban Jami’ar Jos takwas har lahira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jama’a a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato sun shiga jimami a yayin da ɗalibai guda takwas suka rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su da asubahin ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na dare a lokacin da ɗaliban su 11 suke kan hanyar wata tafiya, inda suka yi taho mu gama da wata tirela a daura da Bankin Unity da ke kan hanyar Zariya a Jos, Babban Birnin Jihar Filato.

A cewar Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) reshen jihar ta bakin Kakakinta, Peter Longsan, an samu gawar ɗalibai bakwai a lokacin da jami’ansu suka je wajen da abin ya faru.

Daga bisani mutum ɗaya ya rasu a asibiti, lamarin da ya kai jimillar rashin zuwa takwas. Sauran ɗalibai ukun kuma ana kula da su a halin yanzu.

Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa bos ɗin, wadda ke tafiya cikin yanayi na gudu sama da kima, ta yi yunƙurin kere tirelar ne ba tare da yin hakan bisa nasara ba, lamarin da ya rikita direban da haddasa cin karo da babbar motar.

Kwamandan Shiyya na FRSC, Olajide Mogaji ya ce za su fitar da cikakken bayani akan al’amarin nan ba da jimawa ba.

Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa da su ƙaurace wa tafiye-tafiyen cikin dare, gudu sama da kima, tuƙin ganganci gami da tuƙi a yayin gajiya.

A ƙarshe, ya nemi al’umma da su riƙa tuntuɓarsu ta lamba kamar haka: 122 domin bada rahoton haɗurra ko al’amuran gaggawa da suka shafi kan hanya.

By Babaji