Kungiyar ’yan takarar ADC ta Kano ta gudanar da taron tattaunawa kan cigaban tafiyarsu

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Kungiyar ’yan takarar Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta Kasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Hon. Haruna Yahaya Kadana ta gudanar da taron tattaunawa domin duba matsayin jam’iyyar cigaban da aka samu da kuma kalubalen da ke gabansu yayin shirye-shiryen zaɓen da ke tafe.

A jawabinsa yayin taron Shugaban ƙungiyar Hon. Kadana ya bayyana irin ƙoƙarin da jam’iyyar ke yi wajen ƙarfafa tsarin ta da tabbatar da cewa tafiyar siyasar ADC ta samu gagarumin ci gaba a Kano. Ya ce jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a wuraren al’umma daban–daban.

Ya kuma bayyana cewa kwanan nan sun kai ziyara Jihar Adamawa domin halartar babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda ya bayyana yadda aka samu nasarar haɗa kan ’yan takarar jam’iyyar da suka tsaya a zaɓen da ya gabata. 

Hon. Haruna ya ce irin wannan haɗin kai na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa jam’iyyar gaba ɗaya.

Hon. Kadana ya jaddada cewa ƙasar nan da ma Jihar Kano na fuskantar manyan matsalolin tattalin arziki da zamantakewa wanda hakan ke buƙatar jajirtattun shugabanni domin dawo da jihar kan hanyar ci gaba.

“Mun sani cewa kasa na cikin buƙatar ɗauki, domin samar da mafita ga ƙalubalen da ke hana al’umma cigaba a Kano da ma kewayenta.

“Tafiyar nan na ƙara samun karɓuwa sosai, domin al’umma na ƙara tururuwa suna neman zama cikin wannan tafiya ta canji.”

Ya ce babban burinsu shi ne al’umma su fahimci irin gudummawar da jam’iyyar ke shirin bayarwa, musamman wajen inganta rayuwar matasa maza da mata.

A nasa jawabin, Sakataren Kungiyar ’Yan Takarar ADC Hon.Abba Sagir ya ce wannan lokaci ya nuna cewa akwai bukatar ’Yan takarar jam’iyyar su tashi tsaye wajen fuskantar sauran jam’iyyun adawa da ke fafatawa kafin zabe.

Ya yi nuni da cewa tunkarar ƙalubalen da ake da su a matakin gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu da kuma tasirin manyan ’yan siyasa irinsu Rabiu Musa Kwankwaso, ba ƙaramin aiki ba ne.

A yayin taron’yan takarar sun gabatar da shawarwari daban–daban da kuma manyan batutuwan da ke buƙatar warwarewa domin tabbatar da samun nasara a zaɓen da ke tafe.

By ukarofi