Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sallami zakaran gasar damben duniya, Anthony Joshua daga asibiti bayan wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a babban titin Legas zuwa Ibadan ranar Litinin, wanda ya yi sanadin mutuwar abokansa biyu, wato Lateef Ayodele da Cin Gami.
A wata sanarwar haɗaka daga Gbenga Omotosho, wanda shi ne Kwamishinan Labarai na Jihar Legas da Mai bada Shawara akan Harkar Labarai na Jihar Ogun, Kayode Akinmade, gwamnatocin jihohin biyu sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamatan.
Sun kuma yi musu addu’ar samun rahama tare da fatan juriya ga iyalansu bisa rashin nasu.
Sannan, sanarwar ta tabbatar da batun sallamar Joshua daga asibiti a daren Talata wayewar Laraba, inda suka bayyana yadda ya nuna kaɗuwarsa game da rashin abokan nasa biyu.
Haka kuma, ta ce Joshua da mahaifiyarsa sun je wani gidan ta’aziyya a Legas, inda ake zaman makokin abokan nasa domin jajenta wa iyalai, ƴan uwa da abokan arziƙi.
Kazalika, ta yi godiya ga jami’an lafiyar da suka kula da shi akan iftila’in da sauran waɗanda al’amarin ya rutsa da su.
