Tsohon daraktan DSS na ƙasa, Lawal Daura ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tsohon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Lawal Daura, ya sanar da shirinsa na tsayawa takarar gwamnan Jihar Katsina a zaɓen 2027.

Daura, ya soki yadda gwamnatin da ke kan mulki ke tafiyar da al’amura, tare da nuna matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar jihar a matsayin manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar shiga takarar.

Da yake zantawa da manema labarai, Daura ya bayyana cewa ya kammala tuntuɓa kan burinsa na siyasa, kuma nan ba da jimawa ba zai bayyana jam’iyyar da zai tsaya a ƙarƙashin ta.

Ya ce: “Na daɗe ina yin tuntuɓa kan dandalin da zan yi amfani da shi wajen tsayawa takara, kuma an kammala tuntuɓar. Ba da dadewa ba zan bayyana jam’iyyar.

“Me ya sa mutane ke yin wa’adi ɗaya ko biyu? Idan sun yi abin da ya dace, babu matsala. Amma idan akasin haka ne, to babu dalilin neman sake tsayawa takara.

A bayyane yake gwamnan da ke kan mulki bai da ƙwarewa.

“Kamar ka ɗora kaya a kan mutum kana gyara shi. Idan ya koka cewa kayan sun yi masa nauyi, dole ka sauke su don kada su lalata abubuwa masu rauni.

“Game da gwamnatin yanzu, za mu iya cewa mun gode da ƙoƙarinku, amma ya dace ku huta, domin ba za ku iya ci gaba ba.

“Ban taba ganin kaina zan fito takara ba. Ina sha’awar siyasa, amma kullum ina shiga ne daga bayan fage.” In ji shi.

By ukarofi