“Waƙa saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida”
Daga AISHA ASAS
Shahararre kuma sanannen marubuci da ake alfahari da shi a duniyar Adabin Hausa Khalid Imam, ya samu damar amsa gayyatar jaridar Blueprint Manhaja inda masu karatu za su ji cikakken tarihi tare da nasarorin da ya samu a duniyar rubutu. An dai ce waƙa a bakin mai ita za ta fi zaƙi, ku biyo wakiliyar mu Aisha Asas don jin wane ne Khalid Imam.
MANHAJA: Masu karatu za su so jin tarihinka.
KHALID: Sunana Khalid lmam. An haife ni a shekarar 1973 a unguwar Yakasai da ke cikin Birnin Kano. Ni marubuci ne wanda aka buga wasu daga rubuce-rubuce na a littattafai da muƙalun ilimi a ƙasashen duniya kamar su Amurka da Jamus da Indiya da ƙasar Poland da kuma ƙasar Nepal. Ni mutum ne mai matuƙar sha’awar harkar koyarwa kasancewa ta malamin makaranta na sakandare. Ina da sha’awa sosai a fagen bincike-bincike da kuma rubuce-rubuce. An buga wasu da yawa daga rubuce-rubuce na kamar waƙoƙi ko sharhi a jaridu da mujallu da ke gida Nijeriya na Turanci da na Hausa masu yawa.
Kasancewa ta marubuci na taɓa zama mataimakin shugaban ƙungiyar marubuta ta Nijeriya reshen jihar Kano wato (Association of Nigerian Authors, Kano State Branch). Haka kuma ni ne na kafa kuma na zama shugaban ƙungiyar Dandalin Sha’irai (All Poets Network). A cikin watan Satumba na 2017, na samu halartar wani shiri na musamman a ƙasar Lebanon wanda Jami’ar Notre Dame da Gidauniyar ‘Cedars’ duk na ƙasar Lebanon tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Wole Soyinka ta ƙasar Nijeriya suka shirya wa zaƙaƙuran marubuta goma ‘yan asalin ƙasar Nijeriya don nazarin tarihin duniya da al’ada da adabi da addini. Shi wannan shirin bita na SAIL wato (Study Aboard in Lebanon) ana shirya shi ne da fatan ya ƙara danƙon zumunci tsakanin dukkan ƙasashen da marubutan ta suka amfana da shirin da kuma ita ƙasar Lebanon.
A halin yanzu ni ne Shugaban Kamfanin ‘Whetstone Arts & Translation Serɓices’ kuma Babban Daraktan Makarantar Khalid Imam Academy wadda muke bai wa marayu damar yin ilimi mai inganci a kyauta. Kasancewar ina da sha’awa da kuma ƙwarewa a fagen aikin fassara, haka ta sanya nakan yi aikin fassara ga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa-da-ƙasa kamar su ‘Clinton Health Access Initiatiɓes’ (CHAI) da ‘Mobilising for Deɓelopment’ (M4D) da Mafita da ke ƙarƙashin Adams Smith. Na zama editan mujallu da dama musamman waɗanda ake wallafawa a cikin harshen Turanci. A halin yanzu ni ne editan shafukan adabi na mujallar Turanci ta wata-wata mai suna Platform. Haka kuma ni nake rubuta shafin nan mai suna Sirrin Arziki da Nasara a Mujallar Muryar Arewa wanda take fita a wata-wata.
Na sha karɓar lambobin yabo daga jaridu da hukumomi da ƙungiyoyi masu yawa na gida da wajen Nijeriya kamar su Inuwar Jama’ar Kano da STSB da ANA Kano da PIN da ELTAK. Ina da aure kuma Allah Ya azurta ni da ‘ya’ya maza guda huɗu ga su kamar haka: Khalid (Alhaji) da Shu’aib (Abu Madayyana) da Ahmad da kuma Jamilu.
Ka kasance marubucin waƙa ne kawai ko ka na taɓa wani ɓangare da ba waƙa ba?
A’a, a gaskiya kamar yadda na fara bayyanawa a baya, ni ba marubucin waƙa ba ne kawai. A fagen adabi, zan iya cewa ba ni da gefe duk da cewa wasu sun fi sani na da rubuta wasan kwaikwayo da waƙe, wanda sanadiyyar hakan ne na taɓa zama zakara a fagen gasar rubuta wasan kwaikwayo har sau biyu. A shekarar 2009 na yi nasarar lashe kyautar Tagulla a gasar ƙasa ta rubutun wasan kwaikwayo cikin harshen Hausa da aka shirya don tunawa da marigayi Injiniya Bashir ƙaraye a can Birnin Tarayya Abuja. Kazalika, a shekarar 2010 na sake lashe kyautar Zinare a Gasar Jiha ta Rubutun Wasan Kwaikwayo Cikin Harshen Turanci wanda Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta gudanar don tunawa da Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya.
A fagen rubutun waƙe kuwa, a shekarar 2013 na yi bajintar zama Musulmi ɗan Arewa kuma Bahaushe na farko da ya shiga cikin mashahuran zakaru uku na Gasar ƙasa-da-ƙasa da aka fi sani da Korea-Nigeria Poetry Feast ta hanyar lashe kyautar Tagulla a Gasar Shekara-Shekara a fagen Rubutun Waƙe da harshen Turanci. Har ila yau, a watan Maris na shekarar 2015 na sake samun nasarar zama ɗaya daga cikin mashahuran masu rubuta waƙe da harshen Turancin da aka sake karramawa a wajen wannan gasa ta ƙasa-da-ƙasa ta Korea-Nigeria Poetry Feast da ake yi duk shekara a Birnin Tarayya Abuja.
Wacce shekara ka fara rubutu?
Taɓ! Ai kam dai zan iya cewa na fara rubutu ne tun ina ɗalibi a COE Minna amma dai na fi zaton an fara buga rubutu na ne a jaridar Weekly Trust a shafin su na adabi wanda Ibrahim Sheme ya ke gudanarwa a lokacin a cikin shekarar 1999. Na kuma fara buga littattafai wanda na tattara waƙoƙin ɗalibai na da nake koyawa rubutu a makarantar GTC Ungogo wanda na zama editan sa a shekarar 2004 wato A ‘Citadel of Eɗcellence’ da kuma ‘A Bird’s Eɓidence’ shi kuma a shekarar 2005. Sai kuma na wallafa littafi na na wasan kwaikwayo wato ‘Sodangi’ a shekarar 2009. Sai a shekarar 2010 da na wallafa littattafai biyu da na waƙoƙin Turanci na yabo da nai wa marigayi Sarkin Kano Ado Bayero mai suna ‘The Song of San Kano’ da kuma ‘Letter to my Students’.
Kana ɗaya daga cikin editocin littafin waƙoƙi kan Annobar Korona mai suna ‘Corona Blues’. Faɗa wa masu karatu yadda littafin ya samo asali?
Littafin ‘Corona Blues’ shi ne kundi na farko da aka taskace waƙoƙi da mashahuran marubuta waƙoƙi cikin harsunan Hausa da Turanci suka taru su ka rubuta a Nijeriya. Littafin ƙungiyar ‘All Poets Network’ ce ta yi ƙoƙarin tattara su da buga su tare da tallafin wata ƙungiyar tallafawa ci gaban al’umma da ke a Kano mai suna CITAD tare da tallafin Gidauniyar MacArthur da kuma Cibiyar Tallafawa Ilimi ta Duniya wato ‘International Institute of Education’. Littafin ya samu karɓuwa sosai domin har an gudanar da taro na duniya a kansa a dandalin Zoom wanda Cibiyar Ilimin Kimiyya ta ƙasar Poland wato ‘Polish Academy of Science’ ta shirya cikin farkon watan Afrilu, 2021. Masana daga ƙasashen Jamus da Birtaniya da Amurka da Daular Larabawa da Ghana suka halarta.
Wasu marubuta rubutacciyar waƙa da yawa na ganin duk waƙar da ba ta da ƙafiya ba ta cika waƙa ba. A nazari na ilimi ya zancen yake?
Babu shakka, ƙafiya ɗaya ce daga cikin manyan tubalan gina waƙa ko turakunan dubawa a fagen nazarin rubutacciyar waƙar Hausa kamar yadda wasu masana da manazarta suke faɗi ba don komai ba sai don tana ƙara wa waƙa zaƙi wajen rerawa da saurare ko yi mata kwalliya sosai. Amma inda gizo yake saƙar shi ne ita ƙafiya kayan aro ce. Ba ɓoyayyan lamari ba ne cewa Bahaushe ya aro yin amfani da ƙafiya ne daga sigar yadda Larabawa suke ginin baitocin waƙoƙin su. Cewa waƙa ba ta cika ba sai in har an yi mata ƙafiya a fagen nazari a ilmance ba komai ba ne illa shaci-faɗi. Tabbas babu wani masani ko guda ɗaya da ya taɓa faɗin cewa tilas ne yin waƙa da ƙafiya. Ra’ayi ne kawai na wasu masana cewar waƙa in ba ta da ƙafiya kamar wai ta na da rauni, amma sam ba gaskiya ba ne, wannan ya sanya a fagen nazari a ilmance ake da waƙa da ake kiranta da suna Ballagaza. A fahimta ta yin waƙa da ƙafiya zaɓin marubuci ne abin da ake cewa shan koko ɗaukar wa rai.
Shin haka abin yake a ɓangaren marubuta ko ya abin yake?
Marubuci mutum ne wanda rubutu ya ba shi cikkakken ‘yanci da dama. Shi ƙagaggen rubutu kowanne nau’i tamkar ɗa ne wajen mahaifinsa adabi. Shi ko adabi daji ne ba a yi masa ƙyaure a rufe garam. Wani ko wasu ba sa kallafawa marubuci ƙa’ida wacce tilas wai sai ya bi sannan zai rubutu. Akwai bambanci tsakanin wannan shi ne tsari yadda ake rubuta kaza da kuma cewa wannan ƙa’ida ce tilas sai da ita rubutu kaza ya yi zai zama karɓaɓɓe. Kamar yadda aka sani adabi fage ne na aiki da basira don yin ƙirƙira, shi kuma aikin ƙirƙira ya na bai wa mai basirar yin sa wata irin cikakkiyar dama ta zama ‘yantacce a lokacin da yake gudanar da aikin ƙirƙirar sa. Shimfiɗawa marubuci wasu sharuɗa a ce tilas sai ya bi su, kamar ƙoƙari ne na takure masa basira. Alal misali marubuta kamar masu gina tukunyar ƙasa ne za su iya gina ta duk ta irin sigogi da suka ga dama matuƙar dai a ƙarshe sun samar da tukunya. Haka kuma suna da ‘yancin yi wa tukunyar duk irin adon da suka ga zai fi ƙawata ta ba tare da sai wani ya yi musu tilas ba. Aikin marubuci ya sha bamban da na manazarci wanda sau tari shi akan ɗora shi ne bisa wani tsari don gudanar da aikin binciken sa. Marubuci yana lura da tsari na duk yadda kowanne nau’i ko sigar rubutun kowanne fage yake amma wannan ba ta hana shi haifar da wata sabuwar siga idan yana da sha’awar yin haka tunda dama aikinsa shi ne ƙirƙira. Cewa tilas ne waƙa ba za ta cika ba sai tana da ƙafiya kamar mutum ya ce tilas ne sai da ludayi kawai za a dama fura. Kowa ya sani cewa tsari ne cewa sai an dama ake samar da fura da nono, amma ba tilas ba ne cewa damawar sai da ludayi kaɗai domin ana iya damawa da hannu ko a zamanance a dama da na’urar bilanda da dai sauransu. A gaskiyar magana cewa waƙa rubutacciya ba ta cika sai da ƙafiya kamar cewa ba za a sha fura da nono ba tilas sai da suga. Kowa ya san cewa shan fura da suga shan koko ne ɗaukar wa rai.
Tsakanin rubutun zube da na waƙa wanne ne ya fi wuya?
Za mu ci gaba mako mai zuwa insha Allahu
