UNDP ya nemi a riƙa damawa da mata a harkokin siyasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shirin Ci-gaba na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ta jaddada ƙoƙarinta na bada goyon baya da kira da samar da gyare-gyaren a tsarin dimukraɗiyya ta yadda za a faɗaɗa damarmakin da ake ba dama musamman a harkokin siyasa Nijeriya.

Wakiliyar UNDP a Nijeriya, Ms Elsie Atafuah ta bayyana haka ranar Alhamis a Abuja a wani zaman kwana ɗaya na dabaru akan ƙudirin samar da kujeru na musamman, wato ‘Special Seats Bill’ da Majalisar Ɗinkin Duniya reshen Nijeriya ya shirya.

An gudanar da zaman ne musamman domin ƙungiyar masu fafutukar damawa da mata a harkar siyasa (WPP-PWG) da haɗin-gwiwar matan UN da wasu ƙungiyoyi.

Atafuah ta bayyana cewa taron yana da muhimmanci musamman a wannan lokaci da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ke shirin samar da dokar bai wa mata kujeru na musamman a majalisar.

Ta kuma yaba watan UN, WPP-PWG, Ma’aikatar Harkokin Mata, ƙungiyoyin al’umma da na ci-gaba bisa kira da suke a kodayaushe wajen ba wa mata dama a fagen siyasa.

A cewarta, ƙudirin kujeru musamman na wakiltar wani muhimmin mataki da dimukraɗiyyar Nijeriya da dokokinta ka iya samu, lamarin da zai taimaka wa faɗaɗa haɗin kai da wayar da kan al’ummar ƙasa.

Kazalika, ta ce UNDP zai cigaba da bada goyon baya ga gyare-gyaren a harkokin dimukraɗiyya musamman akan al’amuran da suka shafi mata domin warware matsalolin da aka ɗauki tsawon shekaru ana muhawara akansu.

By Babaji