
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Ministan Abuja Nyesom Wike da ya dakata da shirin tsige Gwamnan Jihar, Ribas Siminalayi Fubara.
A ranar 8 ga watan Junairu ne majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu bisa zargin su da saɓa wa ƙa’idar aiki.
Wannan shi ne karo na uku da ‘yan majalisar suke yunƙurin tsige gwamnan tun bayan zaɓar sa a 2023.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Wike ya zargi Fubara da karya alƙawarin sulhu da Shugaba Tinubu ya jagoranta a tsakaninsu tun a watan Yunin 2025 a lokacin da ya shiga tsakani.
A yanzu, shugaban ƙasar ya sake tsoma baki a al’amarin inda ya umarci da a gaggauta dakatar da dukkan wani yunƙuri na tsige gwamnan, amma bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.
A wani rahoto da gidan talabijin na Arise News ya fitar, Tinubu ya nemi Fubara da ya amine a hukumance cewa Wike shi ne jagoran siyasa a Ribas.
Tun a watan Yunin 2023 ne rikicin siyasa ya ɓarke a tsakanin Wike da Fubara a lokacin da gwamnan ya yi ƙoƙarin yaye kansa daga hannun tsohon mai gidan nasa, lamarin da ya kai ga an samu rarrabuwar kai acikin majalisar dokokin jihar da dakatar da Fubara na tsawon watanni shida.
