Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce, jam’iyyar PDP za ta kawo ƙarshen ƙalubalen da take fama da su tare da neman magoya bayan jam’iyyar da ka da gwiwarsu ta sare.
Ortom ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi a yayin da ya kai ziyara gidan tsohon mai taimaka masa a Makurdi.
Tsohon gwamnan ya ce, ba za ta mutu ba saboda shugabannin jam’iyyar na ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen inganta jam’iyyar a dukkan matakai.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu tana da ƙarfinta, yana mai cewa babbar kwamitin jam’iyyar zai yi zama a ranar Litinin domin tattaunawa.
“Taron da aka yi a Ibadan na wasa ne. Ban taɓa ganin inda kotun tarayya ta yi hukunci amma a dawo a rungumi hukuncin babbar kotun jiha.”
“A bisa doka, mu ne kaɗai aka sahale mana mu tura wa INEC sunayen ‘yan takara da sauransu.”
“Sai dai za mu tara duk wani mai ƙaunar PDP, mu sassanta tsakani da duba yadda jam’iyyarmu za ta samu ci gaba.”
“Za mu yi taron kwamitin gudanarwa gobe (Litinin) ina da tabbacin za mu waraware matsalar rashin gudanar da babban taron jam’iyya da ba a yi ba a jihohi 14.”
“Lallai ne mu gudanar da sauran tarukan da suka rage bayan nan ne kuma za mu yi babban taro na ƙasa,” ya bayyana.
Ortom ya kuma ce dangantakar da ke tsakaninsa da Sanata George Akume, sakataren gwamnatin tarayya shi ne tabbatar da zaman lafiya da halin kan al’ummar jihar.
Tsohon gwamnan ya roƙi shugabannin gargajiya da su guje wa shiga harkokin siyasa da daina ayyana ɗan takarar da suke goyon baya domin a zaɓe shi.
Ya kuma yaba wa tsofaffin masu taimaka masa tare da ba su shawarar cewa su fito fili su bayyana aniyarsu ta tsayawa takara.
A yayin da yake magana, tsohon mai taimaka wa gwamnan, Adzer Abya, ya ce, Ortom ne ya karfafa sarakunan gargajiya a jihar ta hanyar gina fada ga Tiv da O’che Idoma.
“Muna kuma alfahari da irin matakin da ka ɗauka a kan tsaro.”
“Gwamnatinka ta aiwatar da dokar haramta kiwo a sarari da killace dabbobi ta shekarar 2017 wanda ya zama abin tunawa a tarihin jihar nan.”
“ɗaukar wannan mataki ya nuna yadda ka fifita kula da lafiya da mutuncin al’umma sama da siyasa duk da irin matsin lambar da ka sha daga Abuja,” ya bayyana.
Daga nan suka ƙara jaddada goyon bayansu ga tsohon gwamnan da ba shi tabbacin mubaya’a a yayin da suke shiga harkokin siyasa a jihar.
