Hon Khamis ya tallafa wa ɗaliban Dutsinma da Naira miliyan 33

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hon. Khamis ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce tallafin ya shafi ɗalibai 231, waɗanda ke karatu a matakai da fannoni daban-daban a faɗin ƙasar nan.

Hon Mohammed A Khamis ɗan majalisar dokoki a Katsina mai wakilan ƙaramar hukumar Dutsinma ya ce tallafin zai taimaka wa ɗalibai yan asalin mazaɓarsa wajen biyan kuɗin makarantar su.

A cewarsa, a shekarar da ta gabata 2025, an kashe kimanin Naira miliyan 20.8 (₦20,899,000) domin biyan kuɗin karatun ɗalibai 209, waɗanda ke karatu daga matakin SSCE zuwa PhD.

Rabon ɗaliban ya haɗa da PhD 8, MA/MSc 10, Degree 24, NCE 59, Diploma 73, da kuma SSCE 35 kamar yadda ya sanar.

Haka kuma, a wannan shekarar ta 2026, Hon. Khamis ya ce an kashe ƙarin Naira miliyan 12.02 (₦12,020,000) wajen ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 22 a fannonin kiwon lafiya, musamman Pharmacy Technician, X-Ray Technician, da Biomedical Engineering, domin cike giɓin ma’aikatan lafiya a Dutsin-Ma da ma Jihar Katsina baki ɗaya.

Ɗan majalisar ya jaddada cewa wannan tallafi na karatu yana daga cikin muhimman ayyukan da yake ɗauka a matsayin wakilin al’umma, yana mai cewa zuba jari a ilimi da lafiya shi ne ginshiƙin cigaba mai ɗorewa.

Ya ƙara da cewa, baya ga wannan tallafin karatu, yana ci gaba da bayar da gudummawa da tallafi ga ɗalibai da sauran al’umma lokaci zuwa lokaci, a wani yunƙuri na tabbatar da kyakkyawar makoma ga matasa da ci gaban ƙaramar hukumar Dutsin-Ma gaba ɗaya.

By ukarofi