
Ƙungiyar wakilan gidajen jarida ta Kano ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa ta kaddamar da sabon tsarin taimakekeniya (Cooperative Society) tare da ƙaddamar da rabon kayan abinci na watan Ramadan ga mambobinta.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Cibiyar ‘Yan Jarida da ke Kano, inda aka nada manyan mutane a matsayin amintattun na ƙungiyar, ciki har da Farfesa Sule Ya’u Sule, kakakin Gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, da Babbar Sakatariya a Ofishin Majalisar Zartarwa, Hajiya Bilkisu Shehu Mai Mota.
Tsohon Shugaban NUJ a Kano, Kwamared Abbas Ibrahim, ya bayyana muhimmancin ƙungiyoyin taimakekeniya wajen bunƙasa tattalin arziki, yana mai ba da shawarar a riƙa gudanar da harkokin kuɗi cikin gaskiya da tsari.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Wakilan gidajen jaridu ta Kano, Kwamared Murtala Adewale, ya ce gwamnatin jihar ta bayar da tallafin Naira miliyan 10 a matsayin jari na farko. Ya ƙara da cewa an ware kusan Naira miliyan 3 domin sayo da raba kayan Ramadan, inda kowane mamba zai iya cin gajiyar kayan abinci ko haɗin kayan abinci da kuɗi har Naira 100,000 bisa sauƙaƙan sharuddan biya.
Shugaban Kwamitin Amintattu, Farfesa Sule Ya’u Sule, ya ce ƙungiyar za ta taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da kuma ƙarfafa ‘yancin aikin jarida. Sauran mahalarta taron sun yabawa shugabannin ƙungiyar kan wannan mataki da suka ce zai rage wa mambobi wahala.
