Binciken N432: EFCC na neman izinin ci gaba da tsare El-Rufai

Spread the love

A yau Laraba, tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya shafe kwana na biyu tsare a hannun Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) akan tuhumar almundahana, yayin da lauyansa, A.U Mustapha (SAN) ke fafutukar ganin an bada belinsa.

Wasu alamu kuma na nuna cewa hukumar, na neman izinin ci gaba da tsare shi na wani lokaci, domin bashi damar amsa tambayoyin da ake masa.

El-Rufa’i ya kai kansa hukumar ne ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026, da ƙarfe 10 na safe domin amsa tambayoyi kan zarginsa da almundahanar Naira biliyan 432. Kuma da zuwansa ofishin hukumar, masu bincike su ka ci gaba da yi masa tambayoyi.

Wata majiya a hukumar da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce hukumar na neman ƙarin lokacin tsare El-Rufa’i daga wa’adin sa’o’i 48 da doka ta bada na tsare wanda ake bincike.

Lauyansa, Mustapha ya tabbatar wa jaridar PUNCH cewa El-Rufa’i na hannun EFCC, kuma yana bada haɗin kai a binciken da ake yi masa.

Binciken da EFCC ke yi wa El-Rufa’i dai na da alaƙa da rahoton wani ƙaramin kwamitin majalisar dokokin jihar Kaduna da aka kafa a shekara ta 2024 ne, domin bincikar kuɗaɗe, basussuka da kwangilolin da aka bada a zamanin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.

Da ya ke gabatar da rahoton kwamitin, kakakin majalisar, Yusuf Dahiru Leman ya yi iƙirarin cewa kimanin Naira biliyan 423 ne ake zargin an sace karkashin mulkin El-Rufa’i.

By Babaji