Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani sabon rahoto ya bayyana cewa, ’yan ta’addar ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun kafa sababbin sansanoni da maɓoyarsu a yankin Tuba da yake kusa da wurin binciken man fetur na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) a ƙaramar Hukumar Jere ta Jihar Borno.
Rahoton, wanda jaridar The Guardian ta wallafa, ya nuna cewa, majiyoyi daga yankin da kuma manoma a ƙaramar Hukumar Jere sun tabbatar da cewa an ga kusan babura 200 a wani sansani da ake zargin ’yan ta’addar suke amfani da shi a arewacin jihar ta Borno.
Binciken ya kuma nuna cewa, ’yan ta’addar sun mayar da hankali kan wurin da kamfanin NNPCL ke gudanar da binciken mai, tare da wasu ƙauyuka da garuruwa da ke kusa da su kamar Dusuman, Ngom, Jabarman, Gongulong Lawanti, Koshebe da kuma gefen Muna Garage, wuri mai nisan kusan kilomita 20 gabashin Maiduguri.
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa wasu wuraren da suke kai wa hari sun hada da Madinatu, kasuwar shanu ta Maiduguri, da kuma matafiya da direbobin da ke amfani da hanyoyin Maiduguri zuwa Monguno da Maiduguri zuwa Mafa.
Majiyoyi sun ƙara da cewa ƙungiyoyin ta’addar sun aike da ƙananan rundunonin maharan da ke amfani da babura zuwa yankin Ngom da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Dikwa. Daga nan sai su ratsa zuwa hanyar Maiduguri–Mafa mai nisan kilomita 40, kafin su isa ƙaramar hukumar Konduga a gefen kudancin Sambisa Forest, wacce ta daɗe tana zama babbar mafakar ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Wani mafarauci mai shekaru 65 da aka bayyana da suna Konto Aliyu ya nuna damuwa matuƙa kan barazanar tsaro da waɗannan sabbin maɓoyar ’yan ta’adda ke haifarwa ga al’ummomin yankin.
Ya yi kira ga Kwamandan rundunar Operation Haɗin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, da ya ɗauki matakin gaggawa domin lalata waɗannan maɓoyar a yankin Jere, domin rage ƙarfin ’yan ta’addar wajen kai hare-hare kan sansanonin sojoji da ƙauyukan da ke kewaye.
Rahoton ya kuma nuna cewa a makonnin baya-bayan nan ’yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sun ƙara tsananta hare-hare kan al’ummomi da sansanonin sojoji, lamarin da ya yi sanadin mutuwar kwamandojin rundunar sojin Nijeriya uku.
Masana harkokin tsaro na ganin cewa kafa sabbin sansanonin ’yan ta’adda a kusa da wuraren binciken mai da manyan hanyoyi na iya ƙara jefa yankin cikin matsanancin barazanar tsaro, musamman idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
