Gidauniyar Alin Kano ta shirya taron buɗa-baki domin tunawa da Marigayi Abdullahi Alin Kano

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano 

Gidauniyar Alin Kano Foundation, wacce aka kafa domin tunawa da Marigayi Hon. Abdullahi Alin Kano (Garkuwan Tsakuwa), ta shirya wani taron shan ruwa karo na farko domin tunawa da marigayin tare da yi masa addu’o’i.

An gudanar da taron ne a Makarantar Koyon Fasahar Tuƙi ta ƙasa da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, a ranar Lahadin da ta gabata, inda jama’a da dama daga sassa daban-daban suka halarta.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Kwamared Shafiu Usaini Inuwa, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tunawa da irin gudunmawar da marigayin ya bayar ga al’umma tun yana raye.

Ya ce lokacin da marigayin yake raye, shi ne ya assasa wannan shan ruwa da ake yi a duk ranar 19 ga watan Ramadan, domin hada kan jama’a da kuma gudanar da ayyukan alheri.

“A yanzu duk da cewa ba ya raye, mun ga ya dace mu ci gaba da gudanar da wannan taro domin tunawa da shi tare da yi masa addu’o’i,” in ji shi.

Shafiu Usaini ya kuma nuna farin cikinsa kan yadda jama’a da dama suka halarci taron, tare da bayyana marigayin a matsayin mutum mai son zaman lafiya da hadin kai.

Ya ce marigayin ya kasance dan siyasa wanda ba ya nuna bambancin jam’iyya a harkokinsa, domin a cewarsa burinsa a koda yaushe shi ne hadin kan al’umma da ci gabansu.

Haka kuma ya tabbatar da cewa gidauniyar za ta ci gaba da shirya irin wannan taro a duk shekara domin tunawa da marigayin da kuma nuna kauna ga iyalansa da ya bari.

A nasa ɓangaren, daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Faisal Abdullahi Ali, ya nuna godiya a madadin iyalan marigayin ga wadanda suka shirya taron da kuma wadanda suka halarta domin tunawa da mahaifinsu.

Ya ce sun yi matukar farin ciki da wannan shiri, yana mai cewa mahaifinsu ya bar kyakkyawan tarihi da abin koyi da zai ci gaba da anfani ga al’umma.

Shi ma Hon. Abba Muhammad (Mai Foundation), wanda yana daga cikin abokan marigayin da suka riƙa tafiyar da harkokin siyasa tare, ya bayyana ranar a matsayin rana mai muhimmanci da tarihi domin tunawa da irin gudunmawar da marigayin ya bayar.

Ya ce marigayin ya kasance mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda a koda yaushe burinsa shi ne ci gaban al’umma da zaman lafiya.

A yayin taron, malamai da dama sun gabatar da hudubobi da nasihohi, ciki har da Babban Limamin Dawakin Kudu, Sheikh Umar Tijjani Umar, da Dr. Muhammad Tahir Abdullah, da sauran malamai.

Malaman sun bayyana marigayin a matsayin dan siyasa na gari wanda ba ya nuna bambancin jam’iyya ko siyasa a mu’amalarsa da jama’a.

Sun kuma yi kira ga ‘yan siyasa da shugabanni da su yi koyi da irin halayen marigayin na gaskiya, hadin kai da son ci gaban al’umma.

A ƙarshe, malamai sun yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya kuma ba shi rahama da Jannatul Firdausi, tare da nuna godiya ga wadanda suka shirya taron tunawa da shi.

By ukarofi