Congo za ta karɓi baƙin haure da Amurka ta kora a wannan mako

Spread the love

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo na shirin karɓar fiye da mutane 30 da Amurka ta kora daga ƙasarta a wannan mako, a wani sabon salo da Washington ke amfani da shi na haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka wajen sarrafa batun baƙin haure.

Majiyoyi sun ce waɗanda za a kawo ba ’yan Congo ba ne, kuma wasu daga cikinsu sun fito ne daga Amurka ta Tsakiya da Kudanci.

Ana sa ran adadin zai kai tsakanin mutane 37 zuwa 45.

Za a sauke su a Kinshasa kafin a kai su wani otel kusa da filin jirgin sama, inda za su zauna na tsawon kwanaki 10 zuwa 15.

Wannan mataki ya jawo suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da ’yan adawa a Congo, musamman ganin cewa ana kai mutane zuwa ƙasar da ba tasu ba.

Amurka ta taɓa yin irin wannan a ƙasashe kamar Ghana, Cameroon da Eƙuatorial Guinea.

Wasu daga cikin waɗanda aka kora sun taɓa samun kariya daga kotuna a Amurka, amma daga baya aka mayar da su ƙasashensu.

Rahotanni sun ce za a basu ɗakuna daban-daban, tare da abinci sau biyu a rana, kuma za su iya fita da zirga-zirga cikin ’yanci.

’Yan sandan Congo da kamfanonin tsaro masu zaman kansu za su kula da tsaron wurin.

Kungiyar IOM za ta taimaka musu bayan isowarsu, duk da cewa ba ta da hannu kai tsaye a aikin korar.

Wasu daga cikin waɗanda aka shirya korarsu sun fito daga Colombia, Peru, Chile da Guatemala.

Har yanzu ba a bayyana abin da zai faru da su bayan kwanaki 15 ba.

By ukarofi