Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya umarci sojoji a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma da su ƙara yawan hare-haren da ake kai wa ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, yana mai cewa dole ne a tabbatar da tsaron Najeriya ko ta halin ƙaƙa.
CDS ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Jihar Zamfara yau Litinin.
A cewar sa ziyarar ta kasance don tantance shirye-shiryen yaƙin da sojoji suke yi da ‘yan ta’adda, sauraron ƙalubalensu, da kuma basu ƙwarin gwiwa yayin da suke ƙara ƙaimin yaƙi da ‘yan bindiga da satar mutane a duk faɗin yankin.
Ya cigaba da cewa matsin lamba mai ɗorewa ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka zai dawo da tsaro ga al’ummomin da abin ya shafa a jihar da sauran Jihohin Arewacin maso Yamma.
“Kirana shine, sojoji shi ne su fita su kawar da duk waɗannan masu aikata laifuka”. Ya ce
“Dole ne mu tabbatar da tsaron Najeriya a kowane hali,” in ji Janar Oluyede.
Oluyede ya bayyana cewar Gwamnatin Tarayya tana aiki don faɗaɗa ƙarfin rundunar sojan sama ta Najeriya.
Babban hafsan tsaron ya yaba wa Gwamnatin Jihar Zamfara da mazauna yankuna saboda tallafawa ayyukan soji, yana mai lura da cewa sayen motocin sulke na baya-bayan nan dake da ƙarfin Mine-Resistant Ambush Protected (MRAP), ya inganta ingancin fagen daga.
Ya yi kira da a yi haɗin gwiwa mai zurfi daga al’ummomin yankin, yana mai jaddada cewa bayanan sirri masu inganci a kan lokaci suna da mahimmanci don wargaza hanyoyin sadarwa na ‘yan bindiga a Jihar.
Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Operation Fansan Yamma ita ce rundunar haɗin gwiwa ta hedikwatar tsaro wadda ke haɗa sojoji ƙasa, sojojin sama, da sauran hukumomin tsaro don yaƙi da ‘yan bindiga da ta’addanci a faɗin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kebbi, da sassan Jihar Neja.
Ziyarar CDS ta zo ne a daidai lokacin da ake sabunta hare-haren soji da kuma buƙatar samun bayanan sirri daga jama’a don samun ingantaccen kariya ga al’ummomin karkara da manyan hanyoyi a Arewa maso Yamma.
