Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da yake ƙaddamar da sayan takin zamani buhu 400,000 ga manoma a garin Malumfashi.
Gwamna Raɗɗa ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta sayar da takin ne a farashi mai rahusa na Naira 25,000 ga kowane buhu. Wannan farashi, wanda shine kwatankwacin rabin farashin da ake sayar da takin a kasuwannin, wanda hakan ke nuna cewa gwamnati ta ɗauki nauyin biyan kashi 50 cikin 100 na kuɗin domin sauƙaƙa wa manoma da ƙarfafa samar da abinci.
Gwamnan ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na uku da gwamnatin sa ke ƙaddamar da rabon taki gabanin lokacin damuna, ya kuma jaddada cewa wannan mataki na ɗaya daga cikin muhimman manufofin gwamnatinsa na bunƙasa harkar noma da tallafa wa rayuwar manoma a fadin jihar Katsina baki ɗaya.
“A wannan karon, an tsara tsarin rabon takin ne ta yadda zai isa ga ainihin manoman karkara ta hanyar Shirin Ci gaban Al’umma (CDP). Za a raba takin ne kai tsaye zuwa kowace rumfar zaɓe a dukkan mazaɓu guda 361 a faɗin jihar maimakon tsayawa a matakin ƙaramar hukuma ko mazaɓa, domin tabbatar da adalci da kauce wa katsalandan ɗin yan banga-banga, cewar Gwamnan.
A nasa jawabin, Shugaban Shirin CDP, Dakta Kamaladdeen, ya yi bayanin cewa an rarraba takin ne bisa la’akari da yanayin noman kowane yanki, inda Shiyyar Funtua za ta karɓi buhu 60 ga kowace rumfa saboda yalwar noma a yankin, yayin da shiyyar Katsina za ta samu buhu 50, ita kuwa shiyyar Daura za ta samu buhu 45 ga kowace rumfa.
Ya kuma bayyana cewa; baya ga batun taki, haka kuma gwamnati ta raba famfunan ban ruwa guda 4,000 tare da samar da magungunan feshin kwari a lokacin noman rani, Haka kuma, ya ƙara da cewa ana ci gaba da gina rijiyoyin ban ruwa guda 3,000 a faɗin jihar don tabbatar da cewa harkar noma ba ta tsaya ba ko da bayan damuna.
Kwamishinan Noma, Hon. Aliyu Zakari Shargalle, da shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi, Hon. Muntari City, sun yaba da wannan ƙoƙari na gwamna, inda suka bayyana cewa wannan shiri zai taimaka ƙwarai wajen tabbatar da wadatar abinci da bunƙasa tattalin arzikin jihar Katsina.
