
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya magantu bayan wani al’amarin firgici ya auku a kusa da Fadar White, inda ya bayyana halin da ya tsinci kansa aciki a matsayin “aiki mafi wahala”, bayan faruwar abin da hukumomi suka kira da yunƙurin kisan kai da gangan.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai sa’o’i bayan faruwar al’amarin, Trump ya bayyana cewa wani da ake zargi ɗan bindiga ne ya kutsa wa shingen binciken jami’an tsaro kana daga bisani jami’an leƙen asirin ƙasar suka daƙile harin nasa.
Rahotanni sun bayyana cewa, gaggauta fitar da Trump ne tare da matarsa Melania Trump daga wajen taron na cin abincin dare na shekara-shekara na wakilan Fadar White House da aka saba yi a Birnin Washington D.C a ranar Asabar a lokacin da wani ɗan bindiga ya buɗe wuta ana tsaka da shagali.
Al’amarin ya faru ne a daidai wajen da jami’an tsaro ke tantance mahalarta, inda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa tare da buɗe wa jama’ar wajen wuta.
Haka kuma, wani jami’in sirri ya tsallake rijiya da baya bayan harbinsa da aka yi a lokacin da yake sanye da rigar kariya.
Tuni dai jami’an tsaron da ke wajen suka hanzarta fitar da Shugaba Trump da matarsa da wasu manyan jami’an gwamnati daga wajen yayin mutane sama da 2,600 da suka halarci taron suka shiga cikin firgici.
Kazalika, an ga yadda baƙin suke fakewa a ƙarƙashin teburan da aka jera yayin da jami’an tsaron suka yi ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali da lumanar al’umma.
Daga cikin waɗanda jami’an suka tilasta wa ɓuyar akwai manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da: Sakataren gwamnati, Marco Rubio; Sakataren Lafiya, Robert F. Kennedy Jr.; da kuma Sakataren Harkokin Cikin Gida, Doug Burgum.
