Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Shahararren ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa a fannin ma’adinai a jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya, Alhaji Abdullahi Adamu Danchina, ya bayyana kudirinsa na ci gaba da shiga harkokin siyasar Nijeriya domin taimaka wa al’umma su samu abin yi, ingantacciyar rayuwa da kuma tsaro.
Danchina ya bayyana hakan ne a garin Narabi yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce halin da Nijeriya, musamman yankin Arewa, ke ciki a halin yanzu abin tausayi ne.
Ya ce a kullum yana shiga daji domin aikin haƙo ma’adinai, inda ake yawan kiransa ba ƙaƙƙautawa don neman kayan da yake samarwa daga ƙasa. Ya ƙara da cewa, bayan ya fitar da ma’adinan, ana lodawa a manyan motoci zuwa tashoshin jiragen ruwa domin kai su ƙasashen waje.
A cewarsa, wannan sana’a tana biya masa buƙatu, kuma tana ba shi damar taimaka wa mutane ba tare da la’akari da bambancin ƙabila ko addini ba.
Ya jaddada cewa dukkan ayyukan siyasa da yake yi na da nufin taimaka wa jihar Bauchi. Ya ce idan Allah ya ba shi dama ya zama gwamna, zai yi amfani da arzikin ma’adinai da ke jihar wajen samar da kuɗaɗen shiga, ta yadda za a iya biyan albashi da gudanar da ayyukan raya kasa ba tare da jiran tallafin gwamnatin tarayya ba.
ɗanchina ya kuma buƙaci talakawan Nijeriya da su kasance masu lura wajen zaɓen shugabanni nagari da za su fitar da su daga halin matsin tattalin arziki da rashin tsaro.
Ya ƙara da cewa ya kamata kowa ya tashi tsaye ya nemi abin yi domin dogaro da kai, tare da gujewa kabilanci da nuna bambanci, domin hakan ne zai taimaka wajen samun nasarar siyasa da kuma gudanar da zaɓe cikin lumana a shekarar 2027.
A ƙarshe, ya ja hankalin ‘yan takarar gwamna da na shugaban ƙasa da su daina tunanin cewa za su samu kuɗi a baitulmalin gwamnati idan suka hau mulki. Ya ce a halin yanzu ƙasar na fuskantar matsin bashi daga ƙasashen waje da cibiyoyin lamuni, lamarin da ke nuna cewa dole ne a nemo hanyoyin cikin gida na bunƙasa tattalin arziki.
Ya jaddada cewa idan aka zaɓe shi gwamnan jihar Bauchi, zai mai da hankali kan haɓaka fannin ma’adinai, wanda a cewarsa zai iya samar da kuɗaɗen shiga fiye da man fetur, tare da samar da ayyukan yi da rage talauci a tsakanin al’umma.
