Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata mummunar guguwa ta lalata gidaje sama da 1,200 a wasu al’ummomi da ke jihar Neja.
Babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Kwamared Abdullahi Baba Arah, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayar da rahoton halin da ake ciki ranar Alhamis a Minna.
A cewarsa, guguwar ta yi ɓarna a ƙananan hukumomi shida na jihar da suka haɗa da Mokwa, Bida, Laɓun, Katcha, Gbako da Mariga.
Ya ce hukumar NSEMA ta fara gudanar da bincike cikin gaggawa domin tantance irin ɓarnar da guguwar ta yi da kuma buƙatun jinƙai na mutanen da abin ya shafa.
Arah ya bayyana cewa rahotannin farko sun nuna cewa sama da gidaje 1,000 ne suka lalace ko suka rushe gaba ɗaya a wasu yankuna na ƙaramar Hukumar Mokwa, ciki har da Sawmill, Kpege Wayata, Kpege, Station Girigi, Efu Shaba Lile, Tifin Madza, Yafu, Etisheshi, Hakimi Aliyu da yankin Nasfat.
Haka kuma, ya ce a ƙaramar Hukumar Bida, guguwar ta shafi yankunan Cheniyan, Nasarafu, Bariki, Kyari, Dokoza, Masaga A da Masaga B.
Ya ƙara da cewa an kuma samu irin wannan ibtila’i a ƙananan hukumomin Laɓun, Katcha, Gbako da Mariga, inda tun farko aka ruwaito lalacewar gidaje sama da 100 a ƙauyen Durgu da ke yankin Bobi na ƙaramar Hukumar Mariga.
A cewarsa, hukumar NSEMA tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki da hukumomin ƙananan hukumomi na ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano girman ɓarnar da kuma irin taimakon da waɗanda abin ya shafa ke buƙata.
