Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Nijeriya da Amurka sun halaka mayaƙan ISWAP 20 kwanaki kaɗan da kisan kwamandan ISIS

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojojin Nijeriya da ke aiki da haɗin-gwiwar Sashen Dakarun Tsaron Amurka a Afirka (AFRICOM), sun ƙaddamar da sabon hari akan ‘yan ta’adda, inda suka yi nasarar halaka samar da mayaƙan ƙungiyar ISWAP guda 20 a Jihar Borno.

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce harin ya auku ne a maɓoyar ‘yan ta’adda da ke Metele a arewacin jihar, yankin da ke fama da hare-haren mayaƙan a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

Manjo-Janar Samaila Uba, Daraktan yaɗa labaran hedikwatar, ya sanar da haka a wata takarda, ranar Litinin.

A cewar hedikwatar, an ƙaddamar da harin ne bayan samun wasu bayanai na sirri da ke bayyana yanayin zirga-zirga da taruwar ‘yan ta’adda a yankin.

Akan haka ne dakarun tsaron suka yi wa mayaƙan ruwan wuta ta sama, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da ‘yan ISIS/ISWAP guda 20.

Manjo-Janar Samaila Uba ya bayyana cewa atisayen, wani ɓangare ne na ƙoƙarin kassara tsare-tsaren ‘yan ta’adda da lalata dukkan shirye-shiryensu a Shiyyar Arewa ta Gabashin Nijeriya.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da dakarun suka yi nasarar halaka babban kwamandan ISIS, Abu-Bilal Al-Manuki da kuma aka sani da Abu-Mainok.

By Babaji