
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutane biyar na cocin EKWA a garin Omugo da ke Gundumar Oro Ago a Ƙaramar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara da aka yi awon-gaba da su sun rasu a hannun ‘yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa, ministan cocin Reberen Timothy Omole ne ya faɗi hakan a wani saƙon WhatsApp ga mambobin cocin, sannan ya kuma tabbatar wa manema labarai a yammacin ranar Laraba.
Daga cikin wadansuka rasu akwiya matar faston, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole.
Marigayiyar tana ɗaya daga cikin ‘yan cocin guda takwas da aka sace yayin harkokinsu na ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, 2026.
Wannan ya jefa jama’ar cocin cikin jimami musamman ga shugaban, wato Rev. Omole duba da halin da mutanen suka shiga.
A cewarsa, waɗanda aka sace sune Cif David Omopariola, Baba Cif Joseph Ibitoye Afariogun, Mrs. Iyabo Aniyi, Baba Joshua Akanbi Adeyemi da Mrs. Rachael Oluwaremilekun Omole, matarsa.
Da fari, ‘yan bindigar sun nemi a biya su Naira biliyan q kana daga bisani bayan doguwar tattaunawa suka amince a biya miliyan N150.
